Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sashen Hausa Ya Fara Ziyartar Kafafen Yada Labarai A Ghana


Bayan Isar Alhaji Aliyu Mustafa Sokoto, shugaban Sashen Hausa na Murya Amurka zuwa Accra, ya fara da ziyarar tashar talabijin mai suna Hijra TV a ranar Asabar, inda ya samu gagarumin tarbo daga shugaban tashar, Abdul Razak Toure da ma aikatan tashar.

Asma'u Bawa ta yi hira da shi kai tsaye a talabijin, inda ya bayyana makasudin ziyarar tasa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a inganta aikin jarida baki daya da kuma zamantakewar mutane.

Daga Hijira TV tawagar ta Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto ta tafi gidan radio Marhaba 99.3 FM.

ALIYU MUSTAPHA SOKOTO
ALIYU MUSTAPHA SOKOTO

Nan ma Alhaji Aliyu yayi hira da shugaban tashar, Alhaji Baba Shariff akan yadda aikin radio ke tafiya da kuma yadda VOA ke taimaka wa tashar da shirye shiryenta da ake yadawa a tashar tare kuma da zummar inganta huldar da ke tsakanin tashoshin VOA da Marhaba.

Abin da ya kara wa ganawar armashi shi ne hira da Babaa Sharif ya yi da Alhaji Mustapha Sokoto a studio marhaba, inda hira ta kai har ga manufofi da ajenda na voa Hausa.

A karshe an bai wa masu saurare dama, inda suka nuna farin cikinsu da wannan ziyara na shugaban VOA Hausa.

Tuni dai ya shiga birnin Kumasi jihar Ashanti ya wuce zuwa jihar Arewaci inda ya dawo birnin Accra ya sadu da sarakunan Hausawa, sai kuma Sheikh Dakta Usman Sharubutu, sannan yayi bankwana da al’ummar Ghana.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:01 0:00


Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG