Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Jami’ar Yamai Sun Janye Yajin Aikin Da Suke Yi


Hotunan Jama'a a kotu da ke Yamai
Hotunan Jama'a a kotu da ke Yamai

Malaman jami’ar Yamai sun ba da sanarwar kawo karshen yajin aikin da suka shafe wata guda suna gudanarwa da nufin nuna rashin jin dadi game da dukan da suke zargin wasu dalibai sun yi wa wani malamin jami’ar a tsakiyar watan jiya lokacin da wani sabani ya shiga tsakaninsu.

A wata sanarwar da magatakardar kungiyar malaman jami’a reshen Yamai, Mohamman Kabiru Mamman, ya karanto bayan tattaunawar da ta kwashe sa’o’i da hukumomin ilimi mai zurfi, malaman jami’ar Yamai sun yanke shawarar kawo karshen yajin aikin da suka tsunduma a tsakiyar watan jiya saboda abin da suka kira yunkurin azabtar da malamin jami’a.

Malaman jami’ar dai sun daura laifi a akan shugabannin kungiyar daliban jami’ar Yamai, wadanda tuni aka kori biyar daga cikinsu daga jami’ar.

Kungiyar malaman jami’ar reshen Yamai ta bukaci magoya bayanta cewa daga yanzu su dauki dukkan matakan da suka dace domin cike gibin karatun da ya biyo bayan yajin aikin da ya shafe wata guda ana gudanarwa.

A ranar Larabar da ta gabata ne kwamitin mashawarta a jami’ar Yamai ya ba da sanarwar wasu manyan shugabannin kungiyar dalibai daga jami’ar baki daya, saboda zarginsu da yunkurin dukan wani malamin jami’a a farkon watan jiya, lokacin da ya yi kokarin ratsa wani taron ‘dalibai.

Wannan lamarin ya sa malaman jami’ar Yamai tsunduma yajin aiki na sai yadda hali ya yi.

Kungiyar dalibai dai ta kai maganar gaban shari’a, sai dai kotun ta ce daliban ba su da hurumin gurfanar da malamai a kan batun yajin aiki.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG