Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man United Na Dab Da Sayen Dembele Daga Barcelona


Ousmane Dembele

Kungiyar ta Manchester United ta Ingila na dab da cimma daidaito, a fafutukar sayen dan wasan Barcelona ta kasar Spain Ousmane Dembele, a daidai lokacin da ake rana ta karshe ta rufe kasuwar cefanen ‘yan wasa.

United din na bukatar samun dan wasan mai shekaru 23, wanda mafi akasari Barcelonar ke amfani da shi a matsayin canji, domin samar da zabi ga dan wasan ta Jadon Sancho.

Sau daya ya taba buga wasa a kakar wasanni ta bana a kungiyar ta Barcelona a karkashin sabon koci Ronald Koeman, inda ya shiga a matsayin canji a minti na 70.

Ousmane Dembele
Ousmane Dembele

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan dan kasar Faransa, ya amince da yarjejeniya da kungiyar ta United, duk da yake dai kungiyar ta na son shi ne a zaman aro, yayin da shi kuma yake fatan barin kungiyar Barcelona na dindindin.

Tuni dai da kungiyar ta United ta kammala cefanen dan wasan Atalanta Amad Traore akan kudi Yuro miliyan 30.

Traore matashi dan shekaru 18, ya soma taka leda ne a kungiyar Boca ta kasar Italiya, kafin komawarsa Atalanta a shekara ta 2015.

Dan wasan na kan hanyarsa ta komawa kungiyar Parma, a zaman aro, kafin ya koma Manchester United a watan Janairu mai zuwa.

Facebook Forum

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG