A jihar Kano, an gudanar da wani taron kasa da kasa don tattauna hanyoyin ceto kananan yaruka dangin yaren Chadi.
A jiya Talata ne aka fara wannan taron na kwanaki biyu, inda masana kimiyyar nazarin harsuna daga Jami’o'i da cibiyoyin nazarin ilimi mai zurfi daga ciki da wajen Najeriya ke gabatar da Makala.
Cibiyar bincike kan kimiyyar harsuna da fassara ta jami’ar Bayero a Kano, da hadin gwiwar sashen nazarin harsunan Najeriya, da na ketare na jami’ar ne suka shirya taron.
Taron ya maida hankali ne akan batun ceto kananan harsuna da aka fi sani da `yan gidan Chadi, wadanda galibin su ake amfani da su a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar ta wannan bangare.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya yaba da rawar da cibiyar, da kuma sashen koyar da harsunan Najeriya na jami`ar ke takawa wajen bunkasa wannan fannin, ya jaddada cewa malamai da ke nazari akan harshen Hausa da dangoginsa na cikin jerin wadanda ke iya cin gajiyar tsarin tallafi kan bincike da nazari na hukumar TETFUND da ke tallafawa harkokin ilimi mai zurfi a Najeriya.
Jakadiyar kasar Poland a Najeriya, Ms. Joanna Tarnawska, ta ce taron manazarta irin wannan na karfafa dangantaka tsakanin al’umomin kasashe.
Taron ya kunshi bikin karrama Farfesa Nina Pawlak wadda ke koyar da harshen Hausa a Jami’ar Warsaw da ke kasar Poland.
Saurari rahoto cikin sauti daga jihar Kano.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 24, 2021
Har Yanzu Ana Zaman Zullumi A Jihar Kebbi
-
Fabrairu 24, 2021
Rashin Adalcin Gwamnati Ke Sa Mu Yin Garkuwa Da Mutane- Shehu Ragab
-
Fabrairu 24, 2021
Hira Da Wata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Jihar Naija
-
Fabrairu 24, 2021
'Yan Ta'adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankar Rago A Maiduguri
-
Fabrairu 24, 2021
Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Wasu Hare Hare A Maiduguri
Facebook Forum