Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United: Ronaldo Zai Yi Kome


Cristiano Ronaldo

A lokacin da yake murza leda a United, a tsakanin 2003 zuwa 2009, Ronaldo wanda dan asalin kasar Portugal ne ya zura kwallaye 118 a wasannin 292.

Shekara 12 bayan barin Manchester United, dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo zai yi kome zuwa tsohuwar kungiyarsa a gasar Premier ta Ingila.

A ranar Juma’a Ronaldo ya sanar da kungiyar Juventus cewa zai tafi yayin da ya rage masa shekara daya ya kammala kwantiraginsa da kungiyar wacce ta saye shi a 2018 daga Real Madrid.

Rahotanni sun ce ya koma tsohuwar kungiyar tasa ne akan kudi euro miliyan 25.

Tun asali Manchester City ce ta fara zawarcin dan wasan mai shekara 36, amma ta janye kan bayan da rahotanni suka nuna cewa City ta lura hankalinsa ya fi karkata kan United.

Da farko City ta yi tayin sayen dan wasan kan kudi euro miliyan 15 amma Juventus ta ce sai euro miliyan 25.

A lokacin da yake murza leda a United, a tsakanin 2003 zuwa 2009, Ronaldo wanda dan asalin kasar Portugal ne ya zura kwallaye 118 a wasannin 292.

A ranar Juma’a, Manajan Juventus Massimiliano Allegri ya ce Ronaldo ba zai sake bugawa kungiyar wani wasa ba bayan da ayyana cewa zai tafi.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG