Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasashen Duniya Sun Yi Alkawarin Taimakawa Libya Da Dala Bilyan 15


Shugabannin kasashen Duniya a taro da aka yi Parsi gameda Libya, jiya Alhamis.

Tsohon shugaban Libya Moammar Gadhafi yana kira ga sauran magoya bayansa da su yi damara domin gwagwarmaya na lokaci mai tsawo, a yayinda sabbin shugabannin wucin gadin kasar suka hadu da shugabbanin kasashen Duniya a Paris.

Tsohon shugaban Libya Moammar Gadhafi yana kira ga sauran magoya bayansa da su yi damara domin gwagwarmaya na lokaci mai tsawo, a yayinda sabbin shugabannin wucin gadin kasar suka hadu da shugabbanin kasashen Duniya a Paris, wadanda suka yi alkawarin bada tallafin dala milyan dubu 15 kudi da kuma kayan aiki ga gwamnatin wucin gadin.

A wani sako na sauti da aka yada ta tashar talabijin ta dake yada shirye shiryenta cikin larabci, jiya Alhamis, shugaba Gadhafi yace magoya bayansa zasu kaddamarda yakin sunkuru har sai Libya ta kama da wuta bal-bal-bal.

A wani sako da aka daga bisani, tsohon shugaban na Libya ya zargi NATO da kokarin mamaye Libya, daga nan yayi alwashin zasu hana daukar mai daga kasar.Ya kira Sirte, gari da aka haifeshi amatsayin “tungar masu tada kayar baya”, Gadhafi yace ba zasu taba yin saranda ba.

Jiya Alhamis a birnin Paris, Faransa da Ingila da wasu manyan kasashe sun yi alakwarin zasu ci gaba da matakan soji da suke dauka a Libya muddin akwai bukatar haka, amma suka ce yanzu dai abinda aka fi maida hankali akai shine sake gine kasar. PM Ingila David Cameron, da kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton duk sun yi kira ga gwamnatin wucin gadin kasar su kafa gwamnatin da ta kunshi ko wani jinsi, kuma akan tafarkin Demokuradiyya.

Madam Clinton ta gayawa masu halartar taron cewa akwai bukatar MDD ta sassauta takunkumi da aka azawa kadarorin Libya. Ta kara da cewa Amurka ta mika dala milyan dari bakwai cikin dala milyan dubu daya da rabi da MDD ta bada izinin abaiwa gwamnatin wucin gadin.

Ita kuma tarayyar Turai ta bada sanarwar dage takunkumi kan kadarori da cibiyoyin gwamnatin Libya 28, ciki har da tashoshin ruwa, bankuna, da kuma kamfanoni dake aikin makamashi.

XS
SM
MD
LG