Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Taron Tattaunawar Wanzar Da Zaman Lafiya Ya Gudana a Sokoto


Taron Tattunawar Zaman Lafiya a Sokoto.
Taron Tattunawar Zaman Lafiya a Sokoto.

Shugabannin al'umma da addinai da kabilu a jihar Sokoto sun yi kira ga mabiyansu da su zauna lafiya tare da juna domin samar da zaman lafiya a jihar don kauce wa tashin hankalin da ke faruwa a wasu sassan Najeriya.

Shugaban Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar na III, ya bukaci Musulmi da su zauna lafiya da wadanda ba Musulmi ba kada abin da ke faruwa na tashin hankali a wasu wurare ya ja hankalinsu ga yin ramuwar gayya.

Yayi wannan kiran ne a wurin wani taro da shugabannin kabilu mazauna jihar Sokoto da shugabannin mabiya addinin Kirista wanda kuma ya samu halartar sauran shugabannin al'umma.

Bisa ga matsalolin da suka biyo bayan zanga zangar da matasa suka gudanar ta janye rundunar SARS hankulan shugabanni sun karkata akan bukatar yi wa jama'a hannuka mai sanda akan bukatar wanzuwar zaman lafiya cikin al'umma.

Tattunawar Zaman Lafiya a Sokoto
Tattunawar Zaman Lafiya a Sokoto

A wannan taro da ya gudana a jihar Sokoto karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, shugabannin al'umma da addini sun yi kira da babbar murya ga mabiyansu akan zaman lafiya da juna.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar, ya ce matsalolin da ke faruwa a wasu sassan Najeriya na kai hare-hare ga wasu kabilu da fasa runbuna ana satar abinci basu da alaka da addini ko kabilanci don haka jama'a su kula.

Ministan ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Maigari Dingyadi, ya ce abin da ya faru wasu marasa kishin kasa ne suka kitsa shi domin wani nufi da ke gare su.

Dingyadi ya kuma yi kira da a zauna lafiya domin samun cigaba da wanzuwar arziki a jihar.

Shi kuwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce ya kamata a daina saka siyasa cikin harkokin da suka shafi tsaro, lafiya, ilimi, da sauran abubuwan ci gaba.

Tambuwal ya kara da ce yanzu haka gwamnati ta shirya horaswa da gyara tarbiyyar matasan jihar da kuma basu abin da za su yi sana’a.

Tattunawar Zaman Lafiya a Sokoto
Tattunawar Zaman Lafiya a Sokoto

Bishop na mabiya darikar Katolika, Mattew Hassan Kukah, wanda shine shugaban kwamitin wanzar da zaman lafiya na Peace Accord ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa Najeriya fa kasarsu ce duk yadda kasashen waje ke son taimakonsu, idan ta lalace ba za su fi su yin kuka ba.

“Yanzu dai lokaci yayi da ya kamata mu fahimci juna, mu hada hannu mu sake gina kasar mu, fatanmu da addu'ar mu ita ce yanzu an koyi darasi duk da yake ana nuna wasu da laifi amma dai mu hade mu dauka duk laifin mu ne” a cewar Bishop Kukah.

Shugaban Kungiyar Mabiya Addinin Kirista ta kasa reshen jihar Sokoto, Nuhu Iliya, ya ce Kiristoci da ke Sokoto a shirye suke su bayar da hadin kai wajan samun zaman lafiya a jihar.

Ya ce “Zan yi amfani da wannan damar inyi kira akan gwamnatoci su fito da hanyar tuntuba ta yadda jama'a zasu iya gabatar da korafinsu akan abubuwan da ke faruwa kusa da su.”

Har ila yau taron ya ja hankalin shugabanni akan bukatar yin adalci ga shugabancinsu domin shi ne jigo ga samar da zaman lafiya.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG