Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagaita Wuta A Sudan ta Kudu


Shugabannin Sudan Ta Kudu da ke takaddama, sun yi kira ga dakarunsu da su daina fada, wanda ke barazanar wargaza 'yarjajjeniyar zaman lafiya, wadda da ma ke tangal-tangal da kuma gwamnatin hadin kan kasar da aka kafa.

Da ya ke magana a wani gidan rediyon kasar jiya Litini, Mataimakin Shugaban kasa kuma tsohon jagoran 'yan tawaye Riek Machar, ya yi kira ga dakarunsa da su mutunta yarjajjeniyar tsagaita wutar da Shugaba Salva Kiir ya ayyana 'yan sa'o'i kafin nan.

"Ina kira ga duk sojojin da ke fada, da masu kare kansu, da su mutunta wannan yarjajjeniyar kwance damarar, su cigaba da zama inda su ke a halin yanzu, " a cewar Machar a gidan rediyon nan mai suna Eye Radio.

Umurnin kwance damarar da Kiir ya bayar, wanda aka shelanta jiya Litini, ya ce dukkannin bangarorin biyu su daina fada daga karfe 6 na yamma agogon Juba. Umurnin ya ce kwamandoji su ja kunnuwan sojojin da ke karkashinsu, su kare rayukan farar hula da dukiyarsu, su kuma kare duk wata kabilar da ta fuskanci barazana daga sojojin da ke karkashin ikonsu.

Daga bisani, jami'an gwamnati sun umurci sojoji su koma bariki ba tare da bata lokaci ba.

Fada ya cigaba da wanzuwa a fadin Juba a rana ta biyar jiya Litini, Sa'o'i bayan da Kwamitin Sulhu Na MDD ya yi kira ga Shugabannin Sudan Ta Kudu su shawo kan dakarunsu da ke fafatawa da juna. Kwamitin ya kuma yi kashedin cewa ta na yiwuwa a dau hare-haren da ake kaiwa kan farar hula da muradun MDD a matsayin laifukan yaki.

Dubban farar hular da ke cikin kaduwa sun dunguma zuwa sansanonin MDD don su kauce ma fadan da ake yi tsakanin dakarun Kiir da na Machar wanda ya barke ranar Alhamis, kuma wani ganau ya gaya ma Muryar Amurka jiya Litini cewa dakarun Kiir sun yi aman wuta kan sansanin kare farar hulan da MDD ta samar.

A birnin Washington kuwa, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi lale marhabin da tsagaita wutar.

XS
SM
MD
LG