Accessibility links

Masu Kare Hakkin Bil Adama A Najeriya Sun Yi Tir Da Karbar Haraji Daga Mutanen Arewa A Kudu


Yan sandan Najeriya a kudancin kasar.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Network for Justice a Najeriya tayi tir da Allah wadai, da wani yunkuri da akeyi na karbar haraji daga ‘yan Arewacin Najeriya, da sunan yin rejista, a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Shugaban Kungiyar, Dr. Bashir Kurfi ya tattauna da wakilin Muryar Amurka, Umar Farouk Musa dake birnin Abuja inda ya ce zasu kalubalanci wannan mataki a majalisar kasa kuma zasu rubutawa shugaban kasar Najeriya da Gwmnan jihar Ogun kokensu a takarda domin a dauki matakin da zai dakatar da wannan yunkuri.

Dr. Bashir ya ce wannan mataki ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.


Yanzu dai an sa ido domin ganin irin martanin da sarakunan arewacin Najeriya zasu mayar, ko kuma matakan da majalisar kasa wadda za’a aikawa takardan koken zatayi.

Mafi yawancin mutanen dake arewacin Najeriya Hausawa ne da Fulani, kuma akwai kabilu kamar Yarabawa da Igbo a kudancin kasar.

Arewacin Najeriya dai na fama da tashen-tashen hankula daga 'yan kungiyar nan da ake kira Boko Haram, 'yan fashi, masu satar mutane domin garkuwa da su, da kuma tarzomar jami'an tsaro.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG