Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ruwa Da Tsaki Na Neman Hanyar Janyo Hankalin Masu Zuba Jari Najeriya


Shugabar hukumar bunkasa zuba jari a Najeriya (NIPC) Yewande Sadiku, ta ba da tabbacin aiki da hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa wajen samun rage haraji don kara janyo hankalin masu zuba jari su ci gaba da shigowa Najeriya.

A wata ziyara da shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa da mukarraban sa, su ka kaiwa hukumar bunkasa jari, don neman aiki tare tsakanin hukumomin gwamnati, Yewande Sidiku ta bayar da tabbacin ganin an samu nasara.

Duk da hukumar bunkasa zuba jarin ba ta da hurumi kai tsaye na rage haraji, amma Yetunde ta ce duk bukatar hakan za ta turawa hukumomin da lamarin ya shafa, musamman wani kwamiti a ma’aikatar kudi don samun ragin da ma wani lokacin yafe harajin shigo da kaya ga masu zuba jari don su kara karfi kafin a fara cin moriyar ribar su.

Shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa Hassan Bello, ya ce hatta wasu masu zuba jari da a ke ce sun fice daga Najeriya za su dawo don girman kasuwar da ke Najeriya.

Hakanan Bello ya ce kamfanonin dakon kaya na jiragen ruwa na Turai da su ka kara farashin dakon da kashi 400% sun rage kudin da su ka sha matsin lamba.

Hassan Bello ya kara da cewa hukumar sa na shirin kafa tashar teku ta tudu a Ibadan da za ta lashe dala miliyan 100 daga masu zuba jari don rage cunkuson tashar bakin teku ta Apapa.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG