Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakiyar Sakataren Gwamnatin Amurka Ta Kai Ziyara Njiar


Victoria Nuland

A ci gaba da rangadin wasu kasashen Afirka da mataimakiyar Sakataren gwamnatin Amurka mai kula da sha’anin siyasa Ambasada Victoria Nuland ke yi, jami'ar ta yada zango a Jamhuriyar Nijar inda suka gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa a yammacin a ganar Alhamis.

Ambasada Victoria Nuland wacce jakadan Amurka Eric Whitaker ya yiwa iso a fadar shugaban kasar Nijar sun tattauna na tsawon awa kalla guda da shugaba Mohamed Bazoum inda ta ce ta gamsu da wannan ziyara da ta ba ta damar tabo muhimman batutuwan da suka shafi dadaddiyar huldar dake tsakanin Amurka da Nijar.

A cewarta, wannan shi ne karo na hudu da take yada zango a rangadin da ya kawo ta nahiyar Afirka inda ta fara da Afirka ta Kudu da Botswana da Tanzania yanzu kuma tana Nijar domin karfafa hulda a tsakanin Amurka da manyan kawayenta da suka yi fice a fannin mulkin dimokradiya a duniya.

Dimokradiyar Nijar nada karfi sosai duk da irin manyan kalubalen da kasar ke fuskanta. Ta ce a yau mun zanta sosai akan yanayin tsaron da ake ciki tare da yin bitar aiyukan hadin guiwar da suka yi don murkushe wannan matsala.

Ta kara cewa sun tabo fannin tattalin arziki domin kamar yadda aka sani sun kaddamar da wani gagarumuin aiki a karkashin shirin Millennium Challenge Corporation dake karfafa aiyukan noma da samarda wadatar cimaka a Nijar da niyyar yin abubuwa da dama wanda ta wannan hanya kamfanonin Amurka za su zo su zuba jari a nan ta yadda za a sarrafa abubuwan da ake nomawa.

Haka kuma ta ce suna da niyyar gudanar da aiyukan da zasu bada damar samar da wutar lantarki ta hanyar hasken rana, sun kuma yi maganar gudanar da shugabanci nagari, dimokradiya da hakkokin mata .

Shugaban kasa a hirar mu da shi ya nuna kwarai yake mutunta harakar ilimi kuma musamman ilimin mata. Sosai muke goyon bayan irin wanann tsari.

Da yake bayyana matsayin gwamnatin Nijar game da wannan ziyara ta Victoria Nuland ministan harakokin wajen Nijar Hassoumi Mssaoudou ya yaba da abin da ya kira dadaddiyar huldar dake tsakanin kasashen biyu yana mai cewa shekara 60 kenan muke da hulda mai karfi tsakaninmu da Amurka.

A yau ita ce kasar dake kan gaba a jerin wadanda ke tallafawa Nijar a fannin yaki da cutar coronavirus, wanda a baya-bayan nan sun aiko mana tallafin allurar riga kafi fiye da 300000.

Amurka babbar kawace da ke dafa mana a fannin tsaro ta hanyar baiwa jami’an tsaronmu horo suna bamu kayan aiki kowane lokaci suna tare da mu don yaki da ta’addanci. A yaddasuka yabawa dimokradiyar Nijar babban abin alfahari ne inji shi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Mataimakiyar Sakataren Gwamnatin Amurka Ta Kai Ziyara Njiar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


XS
SM
MD
LG