Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekara 61 Da Samun ‘Yancin Kai A Nijar: Abubuwan Da Bazoum Ya Tabo A Jawabinsa Ga 'Yan Kasa


Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)
Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)

Ranar 3 ga watan Agusta Jamhuriyar Nijar ke ta shekara 61 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Faransa.

Albarkacin zagayowar wannan rana shugaba Mohamed Bazoum ya yi wa al’umar kasar jawabi ta kafar rediyo inda ya tabo wasu mahimman batutuwan da suka shafi tafiyar kasar.

Shugaban na cewa watanni 4 bayan da ya hau kujerar shugabancin kasa ya yi ta kokarin ganin ya yi abubuwa a aikace daidai da matsalolin da yake tunanin sune suka fi damun ‘yan kasa.

Ya ce a jawabin da ya yi a ranar bikin rantsuwar kama aiki ya yi bitar kalubalen da kasar ke fuskanta kuma biyu daga cikinsu suka fi daukan hankalinsa wato sha’anin gudanar da al’amuran mulki da sha’anin ilimi.

A watanni hudu 4 da rike ragamar kasa, ya ce sun kara ba shi kwarin gwiwar maida hanakli akan wadanan fannoni biyu.

Ya ce ya ga dacewar bukatar daukan matakan gaggawa akan batun tsaro da ‘yan ta’addan dake shiga kasar daga waje wadanda suka matsa kaimi sosai a tsawon wannan lokaci, abin da ya sa jami’an tsaron suka dage da aikin tsaron kasa ba dare ba rana ta kowace kusurwa.

Mohamed Bazoum ya ce yana kara jaddada aniyar karfafa matakan yaki da cin hanci da farautar baragubin ma’aikata da mahandama dukiyar jama’a da masu kashe mu raba wajen bayar da kwangilar aiyukan gwamnati sata da rashin adalaci a sha’anin tsara jarabawa da gudanar da ita da batun daukan ma’aikatan gwamnati.

Ya ci gaba da cewa kamar yadda ya fada a jawabinsa na rantsuwar kama aiki ilimi shine babban kalubalen dake gabansu. Rauninsa ya sa a yau ake da matsala wajen samun ingantattu kuma wadatattun ma’aikatan da za su baiwa kasar damar samun ci gaba.

Ya kuma ce tsarin karantarwa a kasar na bukatar a sake duba shi kuma haka za a yi domin wannan shine zai ba shi damar cika alkawarin da ke tsakaninsu da ‘yan kasa.

Ya ce hakan ne ya sa ya tattauna da masu ruwa da tsaki a sha’anin makaranta don zakulo hanyoyin da za a tunkari wannan matsala a gwamnatance kamar yadda tuni suka fara daukan wasu mahimman matakai.

Ranar 3 ga watan Agusta wani lokaci ne da akan yi aiyukan dashen itace, amma a bana hukumomi sun karkatar da akalar wannan shagulgulan akan mahimmancinzogale.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Shekara 61 Da Samun ‘Yancin Kai A Nijar: Abubuwan Da Bazoum Ya Tabo A Jawabinsa Ga 'Yan Kasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


XS
SM
MD
LG