Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Ladabtarwar da Za'a Dauka Akan Luis Suarez


Hukumar ta FIFA ta ba Suarez da hukumar kwallon kafa ta kasar Uruguay zuwa tsakar rana yau laraba domin su bayyana matsayinsu

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta fara nazarin matakin ladabtarwar da zata iya dauka a kan dan wasa Luis Suarez na kasar Uruguay, a bayan da ya gantsara ma wani dan wasa na kasar Italiya cizo lokacin da suke kwallo a gasar cin kofin duniya.

Hukumar ta FIFA ta ba Suarez da hukumar kwallon kafa ta kasar Uruguay zuwa tsakar rana yau laraba domin su bayyana matsayinsu tare da duk wata shaidar da suke da ita dangane da wannan lamarin.

A cikin minti na 80 da fara wasan jiya talata, hotunan bidiyo sun nuna alamun Suarez ya ciji dan wasan Italiya mai suna Giorgio Chiellini a kafadarsa ta hagu a lokacin da suke kokawar neman kwallo a gaban gola.

Dan wasan na Italiya ya fadi kasa rike da kafadarsa, sannan ya mike ya saukar da rigarsa domin nuna ma alkalin wasa wani wurin da yayi ja a kan kafadarsa daga abinda yace cizon ne na Suarez.

Sau biyu a baya ana dakatar da Suarez daga wasa a saboda cizo. A shekarar 2010 an dakatar da shi na wasanni 7 a bayan da ya ciji Otman Bakkal na kungiyar PSV Eindhoven. A shekarar da ta shige ta 2013, an dakatar da shi na wasanni 10 a bayan da ya ciji dan wasan baya na Chelsea, Branislav Ivanovic.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG