Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka da Iyalinsa Sun Yi Bikin Kirsimati a Jihar Hawaii


Shugaban Amurka Barack Obama da uwargidansa
Shugaban Amurka Barack Obama da uwargidansa

Shugaban Amurka yayi kira ga amurkawa su tuna da mazan jiya da suka sadakar da rayukansu domin 'yancin kasar

Shugaban Amurka Barack Obama tare da mai dakinsa sunyi shagulgulan bukin Krismeti a Jihar Hawai’i, inda aka haifi Mr. Obama, inda ma sukayi kira ga Amurkawa akan su dinga tunawa da sojojin kasar, da kuma mazan jiya.

Michelle Obama ta bi sawun maigidan nata tana cewa iyalai da yawa sun samu damar yin bukukuwan Krismeti ne saboda sojojin Amurka sunyi sallama da iyalansu kuma sun sadakar da rayukansu domin yiwa kasarsu bauta.

Mr. Obama ya bayyana cewa ganin yadda Amurka ta kawo karshen yakin da take yi a Afghanistan, to yanzu ne lokacin da ya dace a nazarci irin gudunmawar da sojojin Amurka da iyalansu suka baiwa kasar.

XS
SM
MD
LG