Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa da Jami'an Hukumar Hana Shan Miyagun Kwayayoyi Sun yi Gangami a Adamawa


Matasa suna tada hargitsi
Matasa suna tada hargitsi

A kokarin wayar da kawunan matasa dangane da illar dake tafe da shan miyagun kwaya matasa da jami'an hukumar hana shan miyagun kwaya ko NDLEA a takaice sun yi gangami.

Hukumar hana sha ko fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a takaice ta yi taron gangami da matasan Adamawa domin wayar da kawunansu kan illar shan miyagun kwaya.

Sun yi gangamin ne a birane da yankunan karkara na jihar ta Adamawa. Jami'an NDLEA da sarakunan matasa na jihar Adamawa sun kuduri aniyar hada karfi domin yakar sha ko sayar da miyagun kwayoyi domin magance matsalar dake hana iyaye barci.

Mtsalar da ta fi damun matasa iata ce shan kwaya wadda ke sasu yin wasu abubuwan asha. Dalili ke nan da yasa shugabannin matasan suka hada kawunansu su tunkari matsalar.Kamar yadda kwamandan hukumar NDLEA na jihar Adamawa ya tabbatar Alhaji Abdullahi Hassan Zungeru ana samun karin matasan dake anfani da muggan kwayoyi, kuma abun takaici har da 'yan mata. Ya ce tun da aka soma siyasa kananan yara sun shiga shaye-shaye na miyagun kwayoyi. Ya ce a bangar siyasa ake koya masu irin wadannan dabu'un. Kamar na 'yan mata yace sannu a hankali daga zo mu je wani biki ko liyafa a ke koya masu. Ya ce abokanan banza da abokanan yawo su ne suke barinsu a cikin shaye-shaye.

Wani dan jagaliya da ya nemi a boye sunansa ya ce suna sha ne domin su sami lafiya su ji dadin aikinsu. Ya ce idan basu sha ba basa jin dadi amma idan sun sha yana warware masu jiki, su bugu su cigaba da aikinsu. Ya ce sun riga sun saba. Idan basu sha ba ba zasu iya aikinsu ba.

Matasan sun alakanta yawan shan kwayar da su keyi da rashin aikin yi. Idan mutum ya samu abun yi babu yadda zai shiga shan kwaya domin ya yi wasu aika-aika.

Ga rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG