Accessibility links

Wasu 'Yan Fashi da Makami Sun Gamu da Karshensu a Hannun 'Yansanda


'Yansandan Najeriya

Fashi da makami ya zama tamkar ruwan dare ne a wasu sassan Najeriya to amma wasu 'yan fashin sun gamu da karshensu a hannun 'yansanda.

'Yan fashi da makami da suka dade suna cin karensu ba babbaka a arewa maso gabas sun fada hannun 'yansanda a jihar Adamawa.

A wani taron manema labarai da ya kira kwamishanan 'yansanda na jihar Adamawa Mr. Geofrey Okeke ya nunawa 'yan jarida makaman da suka samo daga hannun 'yan fashi da suka cafke. Ya ce sun cafke 'yan fashi da makami fiye da 61kana 16 sun rasa rayukansu a wani musayar wuta da 'yansandan suka yi da su. Haka ma 'yansandan sun gano makamai 67 daga hannun barayin.

Kwamishanan 'yansandan ya ce rundunarsa ta gano wasu motoci 21 da aka sace. Wannan nasarar ta 'yansandan ta biyo bayan hadin kai da bayyanan asiri da suka samu daga mutanen gari. Kakakin 'yansandan DSP Mohammed Ibrahim ya roki jama'ar jihar da su cigaba da basu hadin kai domin su kawar da batagari. Ya ce aikin tabbatar da tsaro ba na hukumar 'yansanda ba ne kawai. Ya ce a duk lokacin da mutum ya ga abun da zuciyarsa bata yadda da shi ba to ya garzaya zuwa wurin jami'an tsaro.

A wani abu na cigaba harkokin kasuwanci a kasuwannin dake tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru sun soma farfadowa. Wasu 'yan kasuwar Mubi da suka sha fama da 'yan fashi da makami sun tabbatar da farfadowar kasuwanci. Ya ce mutane dake bayan gari sun soma yadda cewa akwai tsaro a gari. Mutane sun fara bude shagunansu ba tare da wani fargaba ba.

Gwamnatin jihar ta tashi tsaye domin tabbatar da tsaro da walwala. Gwamna Nyako ya nemi a yi hadin kai domin maido da martabar jihar. Ya ce jama'a su hada kai su tabbatar jiharsu ta cigaba kuma an zauna lafiya.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG