Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Mamaye Wani Babban Titi a Kano


Wasu masu matasa da suka mamaye tituna
Wasu masu matasa da suka mamaye tituna

Dubban matasan da suka mamaye babban titin da ke unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo, sun hana masu shiga birnin Kano domin kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.

Matasa sun haifar da cikoson ababen hawa tare da kawo cikas ga yanayin zirga-zirgar Jama’a akan hanyar shiga birnin Kano daga garuruwan Katsina da Daura da sauran garuruwan arewa maso yammacin birnin Kano.

Dubban matasan da suka mamaye babban titin da ke unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo, sun hana masu shiga birnin Kano domin kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.

Matasan na nuna bacin ransu ne kan zargin cewa wani dan sanda ya harbe wani dan uwansu a unguwar ta Kurna kuma ya mutu bayan an garzaya da shi asibiti. Al’amarin ya faru ne biyo bayan sintirin da ‘yan sandan ke yi a yankin domin tabbatar da doka da oda sanadiyyar tarzomar ‘yan daba a yankin ranar Litinin din da ya gabata.

Matashin mai suna Salisu Rabi'u, wanda dan wasan kwallon kafa ne, ya gamu da ajalinsa yayin da wani dan sanda dake cikin ayarin Jami’an tsaron dake sintirin kwantar da tarzomar da ta biyo bayan fadan ‘yan daba ya harbe shi da bingida. Bayan mutuwar Salisu Rabi’u, wani harbin da dan sandan ya yi ya jikkata wasu mutane guda biyu.

Wasu masu matasa da suka mamaye tituna
Wasu masu matasa da suka mamaye tituna

Wannan lamari ya harzuka matasan yankin da hantsin wannan rana ta Laraba zuwa sallar azahar, inda suka fantsama akan titin Katsina Road domin nuna rashin amincewar su da abin da dan sandan yayi, al’amarin daya haifar da cikoson ababen hawa daya dakatar da zirga zirga a yankin.

Sai dai a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta Kano ta fitar dauke da sa hannun kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Usaini Gumel ya bada umarni kama wannan Jami’I da ake zargin da wannan aika-aika.

CP Muhammad Usaini Gumel
CP Muhammad Usaini Gumel

Sanarwar tace kwamishinan ya kuma kafa kwamitin da zai gudanar da bincike game da lamarin.

Yanzu lokacin wallafa wannan labari, Jami’ai na ciki gaba da kokarin kwantar da hankalin matasan, bayan tabbacin da hukumar ‘yan sanda ta bayar na gudanar da bincike bisa adalci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG