Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Yi Arangama Da 'Yan Sanda A Nkoranza Bayan Kashe Wani Matashi Da 'Yan Sanda Suke Zargi Da Fashi Da Makami


The youth of Nkoranza in the Bono East Region attacked the Municipal Police headquarters
The youth of Nkoranza in the Bono East Region attacked the Municipal Police headquarters

Matasa a garin Nkoranza na jihar Bono ta Gabas a kasar Ghana sun kai hari a kan shelkwatar ‘yan sandan yankin inda suka lalata abubuwa suka kuma bukaci a yiwa wani da ake kira Albert Donko mai shekaru 28 da aka kashe shi yayin da yake tsare a hannun ‘yan sanda adalci.

Matasan sun saki wasu mutane shida da ‘yan sanda suka kama a matsayin masu fashi da makami tare da marigayin.

A cewar shedun gani da ido, zanga zangar da matasan suka yi ta rikide ta zama mummnan tashin hankali a tashar ‘yan sanda suna kalubalantar ‘yan sanda da zargin mutanen da fashi da kuma kashe mutum daya.

Matasan sun ce mutumin da aka kashen ba dan fashi da makamin bane, suna kira a gurfanar da duk wanda ya kashe shi gaban doka.

Masu zanga zangar sun lalata motoci dake ajiye a shelkwatar ‘yan sandan yankin, yayin da wasu karin jami’an tsaro suka isa wurin domin kawo kwanciyar hankali da oda.

Shedu sun ce ‘yan sandan sun yi ta harbin gargadi domin tarwatsa masu zanga zangar.

Tun da fari, matasan sun tare hanyar garin kana suka kona tayoyi kafin lamarin ya kara ta’azzara kana suka wuce zuwa tashar ‘yan sanda suka kai hari a wurin.

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG