Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalolin Da Mata Ke Fuskanta A Najeriya


Taron Da Muryar Amurka Ta Shirya Kan Harkokin Mata

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gudanar da taron zauren VOA da ya saba shirywa a kowane wata a birnin Abuja domin tattaunawa a kan batutuwa da suka shafi rayuwar al’umma da ci gaba kasa da baki dayan zamantakewar jama’a.

Muryar Amurka na kawo masana a fanni da dama da suke fashin baki a kan maudu’I da ake tattaunawa akai, haka zalika taron na Muryar Amurka ya kan tattaro mahalarta daga ma’aikatun gwamnati da jami’an tsaro da masu fafutuka da ma talakawa.

A wannan karo taron zauren VOA, ya tattauna ne a kan matsaloli da mata ke huskanta a bangarori dabam daban na rayuwa. Taron da ya samu halartan mata daga bangarori da dama, ya duba irin matsalolin da mata ke huskanta, kamar rashin basu ingantaccen ilimi, kiwon lafiyar mata masu juna biyu, fyade, auren wuri, tallace tallace da cin zarafin mata a gidan aure da kuma rashin basu mukamai a bangaren siyasa da sauransu.

Hon. Asabe Bilita Bashir ‘yar siyasa daga jihar Borno tana cikin mahalartan taron na wannan lokaci, ta kuma ce mata na huskantar matsaloli da dama a bangaren siyasa. Sai dai ta kara da cewa abin takaici shine ‘yan uwansu mata basu zaben su idan suka tsaya takara, tace sun fi samun kuru’un maza a duk lokacin da suka shiga takara.

Hajia Hauwa Bukar itama ‘yar siyasa ce da ta halarcin taro, tace ta dade tana siyasa amma idan ana raba mukamai bayan an ci zabe, mata basu samun manyan mukaman, lamarin dake sa basu da wani tsairi a sayasance.

Ita kuwa Mariya Ibrahim Baba daga jihar Kano tace tun a gida mata ke huskantar tsangwama da bam banci, inda ake fifita ‘ya’ya maza a kan su mata. Ta ja hankali iyaye cewa ‘ya’ya amana ne a hannun su, saboda haka ida Allah Ya baka ‘ya’ya maza da mata yakamata a basu tarbiya tare.

Ga dai rahoton Hauwa Umar daga Abuja a kan taron:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG