Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalolin RashinTsaro Sun Hana Bikin Cika Shekara 61 Da Samun ‘Yanci Kan Najeriya


A jumma'ar nan Najeriya ke cika shekaru 61 da samun 'yanci daga Burtaniya daga lissafin karbar 'yancin a ranar daya ga watan Oktoba na 1960.

In ba don koma bayan tattalin arziki da tabarbarewar tsaro ba, lokacin kan zama na buki a dukkan birane da kauyuka da ma gudanar da faretin 'yan makaranta.

Turawan sun so mika wa Najeriya mulkin gabanin 1960 amma wasu dalilai da su ka hada da hangen nesa na wasu shugabanni, musamman marigayi Sir Ahmadu Bello, don samun damar yaye dalibai a manyan makarantun boko sun jawo jinkirtawa wanda da tun a wancan lokacin karatu ya samu tagomashi da a yau dai iyaye sun tanada makudan kudi su samu 'ya'yansu su yi karatu a makarantun da ke da malamai da kayan aiki.

Akasarin wadanda su ka yi gwagwarmayar karbar 'yancin kan Najeriya sun riga mu gidan gaskiya sa imma ajalin tsufa ko ajalin kisan gilla, kamar yanda ya faru a juyin mulkin farko da a ka yi a ranar 15 ga watan Fabrairun 1966 karkashin Chukwuma Nzeogwu, inda su Sir Ahamdu Bello, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Ladoke Akintola da sauransu, su ka bar doron duniya.

Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi jawabi gaban zauren majalisar dinkin duniya mai nuna muradu da tasirin Najeriya.

Tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon wanda ya ja ragama tsawon shekaru 9 bayan ture gwamnatin soja ta farko ta Aguiyi Ironsi, kuma ya jagoranci yakin basasa, ya ce mulkin soja su ka yi amma su na sauraron shawara.

Kusan an yi canjaras tsakanin tsawon mulkin farar hula da soja a tsawon shekarun 61 inda farar hula ke neman wuce na soja ma don dadewar wannan sabuwar jamhuriya daga 1999.

Wani abun dubawa shi ne an samu shugabannin Najeriya na soja biyu da su ka rikide zuwa farar hula su ka sake dawowa karaga da su ka hada da Janar Olusegun Obasanjo da Manjo Janar Muhammad Buhari.

Najeriya yanzu na fuskantar kalubalen 'yan awaren Biyafara da kasar Oduduwa da ke son shin su fice daga Najeriya ne ko su ware daga arewa?.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Matsalolin RashinTsaro Sun Hana Bikin Cika Shekara 61 Da Samun ‘Yanci Kan Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


XS
SM
MD
LG