Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Fara Kawance Da Wasu Kasashen Afirka Don Magance Matsalolin Tsaro


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Najeriya tana kawance da wasu kasashen Afirka ta Yamma da wasu kasashe domin saita tsarin kiwo ta yadda watakila hakan zai taimaka wajen magance matsalolin rashin tsaro da kuma habaka arzikin kasashen.

Noma da kiwo abubuwa ne da ke bayar da gagarumar gudunmuwa wajen habaka tattalin arzikin kowace kasa ta duniya.

Wannan bai rasa nasaba da yadda gwamnatin Najeriya take cewa tana bayar da fifiko ga wannan fanni duk da yake matsalolin rashin tsaro na tarnaki gare shi, musamman duba da yadda ake alakanta makiyaya masu yawon kiwo da rashin tsaron.

Wannan taron tattaunawa ne tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar kiwo daga kasashen Najeriya, Nijar da kuma Jamhuriyar Benin akan matsalolin da suka dabaibaye harkar kiwo tsakanin kasashen da kuma lalabo mafita.

Jihar Kebbi ta dauki bakuncin taron kuma gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu shi ne ke jagorantar kwamitin wadata kasa da abinci na gwamnatin Najeriya.

Jihar Sakkwato ma tana shirin kulla kawance da wasu kasashe da zummar habaka harkar kiwo don bunkasa arzikin kasa, a cewar kwamishinan kula da lafiyar dabbobi da bunkasa kiwon kifi, Farfesa Abdulkadir Usman Junaidu.

Masana na ganin da mahukunta na aiwatar da abubuwan da suka tsara da gaskiya da tuni an ceto Najeriya, dama wasu kasashen Afirka, daga matsalolin da suka yi musu tarnaki.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Najeriya Ta Fara Kawance Da Wasu Kasashen Afirka Don Magance Matsalolin Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00


XS
SM
MD
LG