Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan ISWAP Sun Yi Garkuwa Da Kananan Yara 20 a Jihar Borno


Mayakan ‘yan ta’adda sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da kananan yara 20 a jihar Bornon Najeriya, inda ‘yan ta’adda suka shafe sama da shekaru goma suna tada kayar baya, kamar yadda wani shugaban al'umma da mazauna yankin suka bayyana a ranar Juma'a.

Hare-haren na ranar Alhamis a kauyen Piyemi da ke kusa da garin Chibok, inda shekaru takwas da suka gabata mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 a wani harin da ya janyo cece-ku-ce a duniya.

A yammacin ranar Alhamis ne mayakan kungiyar IS da ke yankin yammacin Afirka (ISWAP) suka kai farmaki a garin Piyemi, inda suka kashe maza biyu tare da kwace 'yan mata 13 da maza bakwai, kamar yadda mazauna yankin da shugaban al'ummar yankin suka bayyana.

‘Yan ta’addan ISWAP sanye da kakin sojoji sun fara harbe-harbe tare da farfasa shaguna a kauyen tare da kona gidajen mutane, a cewarsu.

“Sun harbe mutane biyu har lahira sannan suka tafi da ‘yan mata 13 da maza bakwai masu shekaru tsakanin 12 zuwa 15,” wani mazaunin garin Samson Bulus ya shaida wa jaridar AFP ta wayar tarho.

‘Yan ta’addan da suka kai hari daga dajin Sambisa sun yi garkuwa da yara 20 a cikin wata mota da suka kwace daga kauyen suka gudu da su cikin dajin,” in ji Silas John.

Har yanzu dai ba a samu jami’an soji da su ka ce komai ba game da harin. Sai dai wani jami'in karamar hukumar Chibok ya tabbatar da harin ba tare da bayar da cikakken bayani ba. Wani shugaban al’ummar ya kuma yi irin wannan bayani game da harin da kuma yaran da aka sace.

"Wannan harin shi ne na uku a cikin 'yan kwanakin nan kuma yana nuna irin hadarin da kauyukan da ke kusa da Chibok ke fuskanta daga mayakan," in ji Ayuba Alamson, shugaban al'ummar garin na Chibok.

Garkuwar ta ranar Alhamis ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da hare-haren sace-sacen jama’a na neman kudin fansa a kan makarantu a shekarar da ta gabata a jihohin ta da ke arewa maso yammacin kasar.

Kimanin yara ‘yan makaranta 1,500 ne aka kama a shekarar da ta gabata a cikin sace-sacen jama’a guda 20 a makarantun yankin, inda dalibai 16 suka rasa rayukansu, a cewar hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.

Tun bayan da aka yi garkuwa da ‘yan matan makarantar a shekarar 2014 ne sojoji ke jibge a garin Chibok, amma duk da haka ana ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin, inda mayakan ke kai hare-hare daga dazuzzukan da ke kusa da su.

XS
SM
MD
LG