Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mene Ne Muhimmancin Gyaran Kundin Mulkin Najeriya?


Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki a lokacin wani zaman majalisar a ranar 9 ga watan Yunin, 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde - RTX1FRKA
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki a lokacin wani zaman majalisar a ranar 9 ga watan Yunin, 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde - RTX1FRKA

Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kadan daga cikin abubuwan da aka yi wa kwaskwarima, akwai dokar da ta ba matasa damar tsayawa takara a matakai daban-daban ciki har da na mukamin shugaban kasa.

Majalisar dattawan Najeriya ta yi dubi kan wasu kudurori da ke gabanta wadanda aka gabatar da nufin a yi gyara ga wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar.

Daga cikin kudurorin da suka fi jan hankula, akwai wanda zai kayyade adadin shekarun da shugaban kasa zai yi idan ya maye gurbin wanda ya rasu da kudirin yin takara babu jam’iya.

Sauran kudurorin da aka yi dubi akan su har da na neman karin jihohi wanda bai samu karbuwa ba.

Sai dai kudurin da ya fi farin jini, shi ne wanda ya bai wa matasa damar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa da na gwamnoni da na majalisu.

“A da shugaban kasar Najeriya sai ka kai shekara 40 amma yanzu ko kana 35 insha Allahu za ka iya tsayawa ka zama shugaban kasa, da gwamna sai ka kai shekar 35 amma yanzu shekara 30 ne, kafin ka je majalisar wakilai da shekara 30 ne amma yanzu a maida shi 25, amma an bar majalisar dattawa a yadda yake wato shekara 35.” In ji Sanata Abdulaziz Nyako, daya daga cikin wadanda suka goya ma kudirin baya.

“Wato shi canza tsarin mulki ko kuma gyara shi abu ne da ya zama wajibi saboda duniya kullum canzawa take yi kuma dole dokoki su rika canzawa don su tafi da zamani.” In ji Sanata Barau Jibrin, a lokacin da wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta tambaye shi muhimmancin wannan gyara.

A farkon makon nan ne matasa suka yi zanga zangar lumana a Abuja, babban birnin Najeriya domin nuna goyon bayansu ga kudirin rage shekarun da matasa za su iya tsayawa takara a matakai daban-daban.

Sai dai baya ga na neman karin jihohi da aka yi watsi da shi, wani kuduri da shi ma bai samu karbuwa ba shi ne neman a rika bai wa mata kashi 35 na mukamai.

“Yau in aka bari cewa mata za a kawo ba saboda cancanta ba, to zai kawo mana matsala, ya zamanto ko minister ce za a kawo ta ya zama ta cancanta.” In ji Sanata Isa Hamma Misau a hirarsa da Medina Dauda.

Yanzu dai ya rage ne majalisun jihohin Najeriya su amince da wannan sauye-sauye da majalisar dokokin ta yi a matakin tarayya kafin dokar ta fara aiki.

Saurari rahoton Medina Dauda domin jin karin bayani:

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG