Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MOROCCO: Fiye Da Mutum 800 Sun Mutu Sakamakon Wata Girgizar Kasa Mai Karfin Gaske


Girgizar kasa
Girgizar kasa

Mutum fiye da 800 aka tabbatar sun mutu yanzu a sakamakon wata mummunar girgizar kasar da ta abka ma wasu yankunan kasar Maroko da ke da dogayen tsaunuka, kamar yadda Hukumar Kula da Binciken Yanayin Kasa ta Amurka ta tabbatar. 

Da ta ke bayani wa Muryar Amurka, wata daliba, Zarah Halim da girgizar kasar mai karfin maki 6.8 a ma’auni ta rutsa da ita a garin Marakesh, ta ce, ‘’Haka kawai na ji kasa na motsi sai kayan dakin suka yi ta fadowa kasa, ba shiri yayata ta bude mana kofa muka ruga kasan bene muna kuka ba tare da mun san abin da ke faruwa ba, ni na zata ma tashin duniya ne’’

Girgizar kasar dai ta lalata tarin gine-gine da layukan wutar lantarki da na sadarwa a wasu lardunan shida da ke kudancin kasar da suka hada da Al Haouz da Marrakesh da Ouarzazate da Azilal da Chichaoua da kuma Taroudant kamar yadda mahukuntan kasar ta Moroko suka sheda.

Girgizar kasa
Girgizar kasa

Al’amarin na shekaran jiya Juma’a ya auku ne da misalin karfe sha daya da mintunan 11 na dare agogon kasar, ya kuma zo a daidai lokacin da suma wasu ‘yan wasan kwallon kafa na kasashen Burkina Faso da Uganda da kuma Nijar ke wani wąsa na neman gurbi a gasar cin Kofin Kasashen Afrika wato CHAN da za a yi a bana.

Girgizar kasa
Girgizar kasa

Abdou Zada Baraze na daya daga cikin ‘yan wasan kwallon daga Nijar da ya shaida wa Muryar Amurka yadda shi da abokansa suka tsallake rijiya da baya.

A nashi bangaren Ibrahim Tikere dan jarida ne da ke bibiyar gasar kwallon kafar da ya bayyana yanayi na firgici da suka tsinci kai a lokacin aukuwar girgizar kasar da ya ce, a garesu bakon abu ne.

To kawo yanzu dai mutum sama da dari takwas hukumomin kasar suka tabbatar sun mutu, baya ga wasu daruruwa da suka ji rauni da dubban da ke bukatar taimako, sai dai aikin jinkai da aka soma gudanarwa, ya ci gaba da fuskantar kalubale saboda nisar yankunan daga manyan biranen kasar, amma Ministan cikin gidan kasar Abdulwafee Lafteet ya ce, suna duk mai yiyuwa don magance matsalolin da girgizar ta haddasa.

"A yanzu jami'an kiwon lafiya da ‘yan kwana-kwana da na agajin gaggawa duk sun tashi haikan suna aikin da ya rataya a wuyansu na ceton rayuka da agaza wa mutane da kuma tantance yawan asarar da aka tafka''

To bayan girgizar kasar farkon, an kara samun hucinta mai harfin maki 4.9 a ma’aunin Rishta mintuna 19 a tsakani, hakazalika an ji girgizar a biranen Rabat babban birnin kasar da kuma birnin Casablanca.

Girgizar kasa mafi muni da kasar ta Moroko ta taba gani shi ne dai wanda ya lakume rayuka kimanin dubu goma sha biyu a shekarar 1960 a birnin Agadir.

~ Ramatu Garba Baba

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG