Accessibility links

Motar Sojoji ta Samu Hatsari a Arewa Maso Gabashin Najeriya


Sabon babban hafsan hafsoshin tsaron kasa, Air Marshal Alex Badeh

A kokarin inganta tsaro a arewa maso gabashin Najeriya daya daga cikin motocin dake dauke da karin sojoji zuwa arewa maso gabashin kasar ta samu hatsari

Cikin shirin ko ta kwana ne aka kara aika da motocin sulke zuwa arewa maso gabashin Najeriya.

Motocin sun nufi kan iyakar jihar Borno da Adamawa a wani sabuwar damara da yaki da masu tayarda kayar baya.Motocin sulke ne aka tura amma daya daga cikinsu ta samu hatsari akan hanya. Akwai sojojin da suka jikata sabili da hatsarin. Motar sulken dai ta fada cikin wani kogi ne kusa da Madagali. Kodayake babu sojan da ya mutu wadanda suka ji ciwo an kaisu asibiti.

Hukumomin soja a Najeriya sun saba layar kawo karshen matsalar 'yanbindiga. Kwamandan rundunar sojan dake Yola Birigediya Rogers Nicholas yace ba zasu gaji ba da wannan yakin da suke ciki da 'yanbindigan. Yace muna da namu shirin kuma ba zan iya bayyana maka ba. Sai dai akwai kalubalen da muke fuskanta. Al'ummar kauyukan basa bamu labari kan kari yadda zamu shirya mu tunkari 'yan ta'adan.

Duk da nasarar da sojojin suka ce suna samu sun roki mazauna kauyukan su dinga sanarda sojoji kan lokaci. Sanarda sojoji kan kari zai taimakesu da samun nasara.

To sai dai wasu masana suna ganin lokaci yayi da gwamnati zata sake salo domin anfani da karfin soji ba zai haifar da da mai ido ba. Muhammed Ismail yace tun lokacin da aka kafa dokar ta baci a jihohi uku lamarin ya kara tabarbarewa inda ana kara kashe mutane fiye da lokacin da ba'a sa dokar ba. Dokar ta baci da yin anfani da soja ba zasu warware matsalar ba. Yakamata a koma a canza lale a rungumi mutanen nan a san matsalarsu. A koma kan taburin tattaunawa.

Ga rahoto.

XS
SM
MD
LG