Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawara Ta Barke Tsakanin ‘Yan PDP Kan Jayayyar Wike Da Atiku


PDP
PDP

Ana ci gaba da samun baraka a manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya. Ta baya bayan nan da ta tsuduma cikin babbar rigima ita ce PDP wadda takaddamar Atiku da Wike ke girgiza ta.

Muhawara ta barke tsakanin ‘yan PDP kan sabanin da ke tsakanin dan takarar jam’iyyar, Atiku Abubakar, da gwamnan Ribas Nyesom Wike.

Wasu ‘yan jam’iyyar na bukatar Atiku ya bi duk hanyar da ta dace wajen sulhuntawa da Wike inda wasu ke cewa ba lallai sai an yi hakan ba.

Tun lokacin da Atiku ya lashe zaben fidda gwani na PDP a ke samun takun saka kan wanda zai tsayar a matsayin mataimakin dan takara, inda nan da nan bayan da ya ayyana gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a matsayin Mataimaki sai rashin jituwa ya kara tsanani tsakanin sa da Wike, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwanin da alamu karara su ka nuna shi ya ke sa ran zama mataimaki a takarar.

Wike dai a ‘yan kwanakin nan ya fito fili ya nuna sam ba wanda ya yi yunkurin sulhuntawa da shi, ya na mai zargin Atiku da cewa ya nemi goyon bayansa, inda da ya samu nasara sai ya maida shi gugar yasa.

Umar Faringado, na gaban goshin tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya nuna har indai Atiku zai yi tasiri sai ya daidaita da Wike.

Duk da wannan dambarwar dan rajin kare muradun Atiku wato Auwal Ila Wazirin Dundaye, ya ce an sulhunta sabanin.

Don nuna kwarin gwiwa kan babban zabe, Auwal Ila ya sha alwashin har indai Atiku ya gaza cika alkawari to a yanke ma sa hukunci mafi tsanani.

‘Yan siyasa, kama daga na jam’iyyar APC mai mulki zuwa sauran jam’iyyun hamayya da su ka yi fice irin NNPP da LEBA na cewa su na turbar nasara matukar za a gudanar da zabe mai adalci.

Da adalci ko ba adalci ba a taba samun zaben da ba a ruga kotu ba bayan sakamako tun bayan na 1999 sai na 2015 inda shugaba Buhari ya hau gado yayin da tsohon shugaba Jonathan ya taya shi murna.

Saurari cikakken bayani a rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG