Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Gano Masu Daukar Nauyin Yan Ta'addan Boko Haram Guda 96- Lai Mohammed


Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed (Twitter/@FMIC)
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed (Twitter/@FMIC)

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kama mutane 96 da kamfanoni 123 da kuma 'yan kasuwan canji 33 da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta'addanci a kasar.

Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana haka yayin gabatar da bayanan yaki da ayyukan cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba Buhari ke yi a kasar. Yana mai cewa, suna da shaidun da ke nuna cewa wasu daga cikin wadannan mutane da abokan huldar su na da alaka da tallafawa ayyukan ta’addanci a Najeriya

Ministan ya kara da cewa nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin tare da kwace wasu kadarorinsu.

To sai dai a bangare guda akwai matsin lamba ga gwamnatin kasar kan ta bayyana sunayen wadanda ake zargin domin jama'a su sani ya kuma zama ishara ga wadansu, kasancewa har yanzu babu wani bayani bayan kama wasu yan canji bisa zargin su da turawa 'yan Boko Haram kudi, da har yanzu gwamnati ta kasa kai su kotu.

Gwamnatin tarayya dai ta bayyana cewa hukumar leken asirin kudade a Najeriya NFIU ce ta gano mutum 96 masu baiwa 'yan ta'adda kudi, musamman yan Boko Haram da kungiyar ISWAP.

Gwamnati ta kara da cewa NFIU ta bankado mutum 424 dake aiki tare da masu daukar nauyin kamfanoni 123 da kuma yan kasuwan canji 33.

Lai Mohammed yace "Binciken ya taimaka wajen damke mutum 45 wadanda za'a gurfanar ba da dadewa ba kuma a kwace dukiyoyinsu

Idan za’a tuna an damke wasu 'yan kasuwan canji da ake zargi da taimakawa wajen turawa 'yan ta'addan Boko Haram kudi. Daga cikin mutum 45 da aka damke akwai Baba Usaini, Abubakar Yellow (Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida), Ibrahim Shani, Auwal Fagge da Muhammad Lawan Sani, wadanda har yanzu babu amonsu balle labarin halin da suke ciki

Iyalan yan kasuwar canji 45 na jihar Kano da aka damke watanni 11 da suka gabata sun yi kira ga gwamnati da ta sake musu mazajensu ko kuma ta gurfanar da su a kotu. Iyalan wanda suka hada da mata da yara sun kai kuka fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a jiya Alhamis, inda suka bayyana cewa rashin mazajensu da iyayen yaransu ya jefa su cikin mumunan hali.

XS
SM
MD
LG