Malaman sun ce ganawar ta ba su damar bude kofar tattaunawa tsakanin sojojin da shugaba Tinubu da kuma kungiyar ECOWAS.
Jagoran tawagar, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana muhimmancin amfani da tsoffin shugabannin kasa da manyan malamai da a ke mutuntawa a Najeriya da Nijar don samar da maslaha.
Shahararren malamin ya ce da yardar Allah bayan ganawarsu da shugaba Tinubu za a samu matsaya mafi a'ala ga dukkan bangarorin don matakin soja ba zabi ba ne a wannan yanayi.
Da ya ke karin bayani Farfesa Mansour Sokoto ya ce ko da irin karramawar tarba da tawagar ta samu ya nuna an kama hanyar sulhu mai dorewa.
Ta bakin Farfesa Sokoto, shugaban sojan Janar Tchiani ya ba da hakurin rashin ganawa ta kai tsaye da tawagar ECOWAS.
A tawagar akwai Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, Farfesa Salisu Shehu da sauran su.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna