Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 37 Sun Mutu A Italiya A Kan Gadar Da Ta Karye


Gadar Italiya
Gadar Italiya

Hukumomin kasar Italiya sun fada a yau Laraba cewa akalla mutane 37 suka mutu a jiya Talata bayan karyewar wata gada kan watan babbar hanyar garin Genoa.

Mutane da dama sun salawanta yayin da ma’aikatan ceto ke ci gaba da neman mutanen da abin ya shafa a cikin buraguzan bangaren gadar ta yankin Morandi da ta ruguje a lokacin a wani ruwan sama mai tsanani.

Rushewar gadar ta sa motoci da yawa sun abka da mitoci 45 zuwa kasa, yayin da gundayen kankaren simintin gadar kuma ya fada kan gine-ginen wasu ma’ajiyan kayan kamfunna dake karkashin gadar. A cewar hukumomin, dukkan wadanda suka mutun direbobin motocin dake kan gadar ne kuma babu wanda ke gefen gadar da ya mutu.

Ministan sufuri na Italiya Danilo Toninelli yau Laraba ya dora laifi a kan kamfanin dake kula da gadar ne, yana mai cewar kamfanin bata cika aikinta da kayau ba. Toninelli yace gwamnati zata kaddamar da binciken duk sauran gadojin kasar da suka tsufa hade da hanyoyin karkashin kasa da motoci ke bi a fadin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG