Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Zimbabwe: Har Yanzu Tana Kasa Tana Dabo


Komi ya tsaya cik a kasar Zimbabwe yayinda ake jiran hukumcin kotu akan  zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya gabata, wanda shine karon farko ba tare da tsohon shugaba Robert Mugabe ba.

Wata kotu ta dage bikin rantsar da Emmerson Mnangagwa har illa masha Allah saboda ta kalubalance sakamakon zaben da aka yi ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata​.

Everson Wishi, wani dan jam’iyyar ZANU-PF ne, ya ce “Jam’iyyar MDC ta garzaya kotu don kotun ta dakatarda rantsar da Mnangagwa a matsayin shugaban kasa. A lokacin yakin neman zabensa, jagoran jam’iyyar MDC, Nelson Chamisa yayi barazanar hana ruwa gudu a kasar idan har bai ci zabe ba, to a ganina abinda yake yi kenan yanzu.

Hadakar Jam’iyyar adawa ta MDC ta ce dan takarar ta, Nelson Chamisa, wanda ya sami kashi 44 cikin dari na kuri’un da aka kada a hukumance, shine ya lashe zaben.

Wakilai masu sa ido na kasa-da-kasa sun yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana amma kuma sun nuna damuwa akan yanayin da aka gudanar da yakin neman zabe da zaben kansa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG