Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 53 Sun Mutu A Wani Rikicin Kabilanci A Kasar Papua New Guinea


Wasu gawarwaki da ako kwaso
Wasu gawarwaki da ako kwaso

'Yan sandan Papua New Guinea sun ce mutane 53 ne aka kashe a wani rikicin kabilanci a yankin tsaunukan kasar da ke fama da rikice-rikice, wannan shi ne kisan kiyashi na baya-baya da aka gani mai alaka da dadaddiyar takaddama a yankin. 

Kwamishinan ‘yan sandan kasar David Manning a ranar Lahadi ya ce jami’ai da sojoji sun kwaso gawarwakin maza 53.

Ana kyautata zaton an kashe su ne a kusa da garin Wabag, mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso yammacin Port Moresby babban birnin kasar.

Nan take dai ba a bayyana takamaimai yadda kisan ya faru ba, amma ‘yan sanda sun ce an sami rahoton zafafan harbe-harbe a yankin.

Ana kyautata zaton lamarin na da nasaba da rikicin dake faruwa tsakanin 'yan kabilar Sikin da Kaekin.

Kabilun yankin sun shafe shekaru aru-aru suna fada da juna a Papua New Guinea, amma kwararar makamai masu sarrafa kansu sun sa fadan zama da muni.

'Yan sanda sun samu bidiyo da hotuna da aka ce daga wurin da lamarin ya faru suka fito. Hotunan sun nuna gawarwaki jina-jina kwance a gefen titi, wasu kuma jibge a bayan wata babbar motar dakon kaya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG