Accessibility links

'Yan Jarida Na Barazanar Kauracewa Ayyukan Jami'an Tsaro A Jihar Filato

  • Garba Suleiman

Jami'in tsaro a wurin tare ababen hawa a kan hanya

'Yan jarida a Jihar Filato sun ce jami'an tsaro su na neman takura ma ayyukan da suke gudanarwa a game da tashe-tashen hanklulan dake faruwa a jihar.

'Yan jarida a Jihar Filato, sun yi barazanar cewa zasu iya kauracewa dukkan ayyukan jami'an tsaro, musamman na rundunar hadin guiwa ta STF, domin nuna rashin jin dadin abinda suka kira neman takurawar da jami'an tsaron ke musu.

Mataimakin shugaban kungiyar 'yan jarida ta Najeriya a Jihar Filato, Iliya Amos, yace wannan ya biyo bayan harin da aka kai kan kauyen Shonon a karamar hukumar Riyom, inda a bayan sun rubuta labarai sai hukumomin tsaron suka zo su na karyata abinda a cewarsa, "sun gane wa idanunsu."

Yace tilas ne su fadi abubuwan da suke gani domin a yi gyara, don haka karyata su da hukumomin tsaro suka yi, tamkar an mayarda fadan a tsakanin 'yan jarida da jami'an tsaro ne.

Sauran 'yan jaridun da suka yi magana ma sun kushe abinda suka kira rufa-rufar da jami'an tsaron ke son yi.

Sai dai kuma kakakin rundunar tsaro nta hadin guiwa a Jihar Filato, Kyaftin Salisu Mustapha, yace ba su da wata matsala su dai da 'yan jarida.

Kyaftin Mustapha yace a ranar da wannan abu ya faru, ba su ga dan jarida ko guda daya a wurin ba, har zuwa dare lokacin da suka dawo. Don haka babu wanda zai yi ikirarin cewa ya rubuta abinda ya ganewa idanunsa ne alhalin ba ya wurin.

Zainab Babaji ta aiko da cikakken bayani daga Jos.

XS
SM
MD
LG