Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Da Dama Sun Bata Sanadiyar Rugujewar Bene a Nairobi


Benen da ya ruguje a Nairobi babban birnin Kenya

Mutane da yawa sun bace bayan da wani dogon bene ya ruguje a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Jami’an tsaro sun ce dama an riga an fidda kowa daga cikin ginin jim kadan kafin ya ruguje a daren jiya Litinin bayan da aka ga alamar tsagewa a bangaren ginin.

Galibin al’ummar Nairobi su miliyan 4 na zama ne a unguwannin marasa galihu ko na masu karamin karfi.

Da yake ana neman gidaje sosai a birnin, macutan magina a yawancin lokuta sukan kaucewa ka’idodin gini wajen girka gidajensu, abinda ke sa gidajen su yi rauni.

Ko a watan Afrilun da ya wuce, mutane 49 suka mutu a lokacin da wani bene mai hawa shida ya ruguje a arewa maso gabashin birnin na Nairobi bayan wani ruwan saman da aka yi.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG