Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Bakwai Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Jihar Neja


Hadarin Kwale-Kwale Jihar Neja
Hadarin Kwale-Kwale Jihar Neja

Mutane uku ‘yan gida daya na daga cikin mutum bakwai da suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a kauyen Zhigiri da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Nejar Najeriya.

Daga cikin wadanda suka rasu akwai matanin Malam Mu'azu Babangida biyu da daya daga cikin ‘ya’yansa. Ya zuwa yanzu ba a san ko su wanene sauran ba.

An bayyana cewa hatsarin ya afku ne a lokacin da marigayen ke tafiya kauyen Dnaweto domin ziyarar bikin suna a cikin wani jirgin ruwa.

Ya zuwa yanzu dai an gano gawarwakin mutum shida daga cikin kogin, yayin da ba a gano ragowar na bakwan ba. An kuma yi jana’izar wadanda suka mutu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wata sanarwa da kungiyar hadin gwiwar kungiyar Shiroro ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Walis Saba, ta bayyanawa manema labarai a Minna ranar Talata, ta tabbatar da faruwar lamarin.

"Wannan yana daya daga cikin tashin hankali da gina madatsar ruwa ya haifar," in ji Saba a cikin sanarwar, ya kara da kira ga HYPPADEC da "a cikin gaggawa don mayar da martani ga wannan mummunan lamari ta hanyar samar da matakan tsaro ciki har da rigunan ceton ruwa ga mazauna kauyen".

Shi ma da yake magana akan wannan batu, daya daga cikin masu shirya taron matasan Shiroro mai suna Yussuf Abubakar Kokki, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki matuka, inda ya nuna cewa gamayyar kungiyoyin sun gabatar da koke ga gwamnati da dama akan illolin da ke tattare da madatsar ruwar.

XS
SM
MD
LG