Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MYANMAR: Jam'iyar NLD Ta Yi Kira A Sako Shugabanninta


Jami’iyar National League for Democracy a kasar Myanmar ta yi kira a yau Talata cewa a sako shugaban kasar Aung San Suu Kyi da shugaban Win Myint da wasu shugaban a jami’iyar. 

Sanarwar da aka kafe a shafin facebook na zuwa ne wuni guda bayan sojojin kasar suka kwace mulkin kasar kana suka tsare manyan ‘yan siyasa.

A yau Talata hanyoyin kasar na nan fayau amma hanyoyin sadarwar wayoyi da yanar gizo sun kuma fara aiki haka zalika an sake bude bankuna.

Wani rubutu da aka kafa kan titi na goyon bayan Aung San Suu Kyi
Wani rubutu da aka kafa kan titi na goyon bayan Aung San Suu Kyi

Sojojin sun ce sun yi niyar kwace ikon kasar ne tun bara, saboda gazawar gwamnati wurin daukar mataki game da zargin aikata magudi a zaben watan Nuwamba da jami’iyar NLD ta samu gagarumar nasara.

A jiya Litinin ne ya kamata sabuwar majalisa ta fara aiki a kasar .

babu-cikakken-bayani-akan-dalilin-juyin-mulkin-myammar

sojoji-sun-yi-juyin-mulki-a-myammar-

sojoji-sun-yi-juyin-mulki-a-myanmar-bayan-da-suka-kama-aung-san-suu-kyi-da-wasu-jami-an-gwamnati

XS
SM
MD
LG