Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Bashin Da Gwamnati Ta Ciyo Daga Bankunan Gida Ya Kai Naira Tiriliyan 28.43


Gwamnan Babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele
Gwamnan Babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele

Kudaden da bankuna ke bai wa gwamnati ya karu da Naira tiriliyan 3.77 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2023.

Alkaluman da aka samu daga babban bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa jimillar bashi da gwamnati ta samu wanda a karewar watan Disambar 2022 ya tashi daga Naira tiriliyan 24.66 zuwa Naira tiriliyan 28.43tn a karshen watan Fabrairun 2023.

A cewar jaridar Punch, babban bankin na CBN ya bayyana a cikin rahotonsa na ‘Kididdigar Kudi da Lamuni’ cewa bashin ya tashi daga Naira tiriliyan 14.9 a karshen watan Janairun 2022 zuwa N26.65tn a daidai lokacin a shekarar 2023.

A wata sanarwa da babban bankin CBN ya fitar, wani mamba a kwamitin kula da harkokin kudi, (MPC) Aliyu Sanusi, ya bayyana a taron na watan Janairu cewa, ana bukatar tsaurara matakan tkaita yawan bashin ne domin daidaita illolin kashe kudade da suka shafi zabe da kuma yadda ake kashe kudaden da gwamnatin ke son karbo rancen a cikin kasar 2023.

Ya kuma ce manyan abubuwa dake kunshe a yarjejeniyar sirri ta NDA su ne girmar bashi kan gwamnati wanda ya karu da kashi 78.15 (y-t-d) a watan Disambar 2022, wanda hakan ya biyo bayan lamunin da Gwamnatin Tarayya ta Najeriya (FGN) ta samu daga babban bankin kasa (kashi 93.21 bisa dari), bankunan kasuwanci (44.26). kashi dari) da kuma bankunan da ba ruwa a kan rancen su (kashi 79.13).

"Wannan yana nuna cewa tsare tsaren kudi da na tattalin arziki sun ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kan tsadar rayuwa da kayayyaki da kasar ke fama da shi a yanzu," in ji shi.

Wani memba na kwamitin kula da harkokin kudi MPC, Adeola Adenikinju, ya ce, hasashen “Bankin Duniya a kan kudin da Najeriya ke samu a cikin gida zai ragu zuwa kashi 2.9 cikin 100 a shekarar 2023.

XS
SM
MD
LG