Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Fama Da Ficewar Likitoci Da Ma'aikatan Jinya Daga Kasar


Likitoci
Likitoci

Hukumomi sun ce tsakanin likitocin 15,000 zuwa 16,000 ne suka kaura a cikin shekaru biyar da suka gabata. Hakan ya bar kasar da ta fi fice a Afirka da likitoci 55,000 kacal ga al'umma miliyan 220.

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta ce dubban likitoci da ma'aikatan jinya na barin Najeriya duk shekara domin samun fiyayyun damarmaki a kasashen waje. Daga cikin abubuwan da ke sa su ƙaura sun haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, ƙarancin albashi da kuma tsarin kiwon lafiya da komai ya mai yawa.

Hukumomi sun ce tsakanin likitocin 15,000 zuwa 16,000 ne suka kaura a cikin shekaru biyar da suka gabata. Hakan ya bar kasar da ta fi fice a Afirka da likitoci 55,000 kacal ga al'umma miliyan 220.

Yawancinsu su na tattare ne a manyan biranen kasar, amma ga sauran kasar, akwai likitoci biyu kacal ga kowane mutum dubu 10.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya bayar da rahoton cewa, likitoci a Najeriya da ma wasu asibitoci masu zaman kansu suna samun dala 2,000 zuwa dala 4,000 a duk shekara, wato kusan dala 200 a wata.

Gwamnati na duba yiwuwar karin albashin ma’aikatan jinya. Majalisar tana nazarin wani kudirin doka da zai bukaci wadanda suka kammala karatun likitanci su yi aiki na tsawon shekaru biyar a Najeriya kafin su samu cikakken lasisin yin aiki. Kuma wata sabuwar doka ta bukaci ma’aikatan jinya su yi aiki akalla na tsawon shekaru biyu a Najeriya kafin su bar kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG