Accessibility links

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Fararen Hula


Daraktan sashen mulki na rundunar sojojin Najeriya Manjo Janar Adamu Baba Abubakarshi ba bada sanarwar musanta zargin da Amnesty Iternational ta yiwa sojojin tana zarginsu da cin zarafin fararen hula a yakinta da kungiyar Boko Haram.

A taron manema labarai da rundunar ta kira Manjo Janar Adamu Baba Abubakar yace kungiyar Amnesty ta fitar da rahoton ne ranar uku ga watan Yuni ta wannan shekarar inda ta ce sojojin Najeriya na yiwa fararen hula kisan gilla da kuma azubtar dasu.

Yace rundunar sojin Najeriya a matsayinta na wadda take da mutunci da sanin ya kamata dole ne ta mayarda martani. Yace Amnesty ta zargi sojojin da kashe fararen hula har dubu goma sha uku lamarin da ya ce babu kashin gaskiya ciki.

Da a ce sojoji na son boye-boye da basu bada amsoshi ga tambayoyi 37 da kungiyar ta yi masu ba kuma cikin gaggawa. Haka kuma sojoji sun ba kungiyar izinin kai ziyara wurin wadanda ake tsare dasu.

Daga bisani kakakin sojin kasa Kanar Sani Usman Kuka Sheka yace Amnesty ta dauki shekaru hudu tana bincike amma ta bukaci sojoji su basu amsa nan take yanke ba tare da samun zarafin yin nasu binciken ba. Hakan bata yiwuwa musamman idan aka yi la'akari da yanayin aikin soji. Mutane ne sun sadakar da kansu saboda kare kasa da jama'arta, sun bar iyalansu da duk wani abun duniya. Bai dace wani kuma ya zo yana tsangwamarsu ba.

Dangane da tsare mutane Kanar Kuka Sheka yace tabas akwai inda suke tsare wadanda ake zargi da aikata ta'adanci. Yace shi yana zuwa wajen saboda haka zargin da suke yi ba haka ba ne. Ana barin mutanensu da 'yanuwansu suna ganinsu.

Ga Hassan Maina Kaina da karin bayani.

XS
SM
MD
LG