Ministan sifirin sama na Najeriya, Sanata Hadi Sirika, ya bayyanawa manema labarai cewa gwamnati ta daukin wannna matakin ne domin cika alkawari da kuma ganin cewa Najeriya ta shiga jerin kasashe duniya dake da jirage mallakar kasa da kuma inganta kima da darajan Najeriya a idon duniya.
Ya kara da cewa za a shiga yarjejeniya tsakanin Najeriya, da kamfanoni da masu saka jari na duniya kamar kamfanin kera jirage na Boeing da kuma na Airbus, wadanda ake ganin sune gaba gaba a jerin kamfanonin da Najeriya zata shiga yarjejeniya dasu.
Wani mai fashin baki akan sifirin sama Malam Ibrahin Dahiru, ya bayyana mahimmancin da kuma tasirin da wannan tsarin na Najeriya, zai yin a kafa kamfanin jiragen sama na kasa ajerin kamfanonin da zasuyi sifiri a Najeriya.
Kamar yadda Sanata Hadi Sirika, ministan sifirin jiragen sama ya bayyana a ranar 20, zuwa 22,ga wannan wata ne ake sa ran cewa za ayi wani taro na kasa da kasa akan sifirin jiragen sama wanda a rana rake sa ran rattaba hannu akan yarjejeniyar.
Facebook Forum