Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kaddamar Da Mota Mai Amfani Da Wutar Lantarki Ta Farko


Mota Mai Amfani Da Wutar Lantarki Ta Farko a Najeriya
Mota Mai Amfani Da Wutar Lantarki Ta Farko a Najeriya

A karon farko gwamnatin tarrayar Najeriya ta kaddamar da motoci da ke amfani da wutar lantarki  a maimakon man fetur, hakan na zuwa ne Karkashin hukumar da ke sa ido wajen ci gaba da zane-zanen motoci ta kasar wato NADDC.

Kazalika ana sa ran 'yan Najeriya za su ci moriyar nasarorin da aka samu a wannan bangaren na sabunta makamashi a kasar da ake ganin zai taimaka wajan inganta yanayin muhalli.

Wannan ci gaba da Najeriya ta samu, ya sanya ta cikin jerin kasashen da suka rungumi sabuwar fasahar amfani da motocin lantarki karkashin kamfanin kera motoci na Hyundai Kona da Stallion Group.

Babban Darakta hukumar NADDC, Mallam Jelani Aliyu, ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan ci gaba a Najeriya, wannan motar da aka kaddamar ta Hyundai Kona tana aiki da wutar lantarki, kuma ba sai ka saka mata man fetur ko na dizal ba, za ka saka ta ne ta yi caji.

Idan muka duba ci gaban kasar mu Najeriya ba abu ne da mutum daya ko hukuma daya za ta iya yi ba, sai an hada kai da kuma hada karfi, shi ya sa ko wane lokaci mu ke kokarin hada karfi da sauran jami’ai na gwamnati da wasu kamfanoni na kasa” a cewar Mallam Jelani.

Ana sa ran yunkurin nan na samar da motoci masu amfani da wutar lantarki ya maye gurbin motoci masu amfani da man fetur, a wani mataki na rage gurbatar muhalli da kuma kai kasa ga tudun mun tsira.

Shugabanin kamfanin hadaka ta Stallion Group, Gurapf Washed, ya ce dukannin kayayyakin da aka yi amfani da su wajen kera motocin na wutar lantarki ne dari bisa dari.

A yanzu haka motar da ke amfani da wutar lantarkin, itace kan gaba a masana’antun kera motoci na kasashen turai, wanda a halin yanzu farashin kowacce mota daya ya kai Naira miliya 24.

Amma babban daraktan hukumar NADDC ya ce ana kokarin ganin an saukaka wa ‘yan Najeriya don samun damar mallakar motar mai amfani da wutar lantarki.

Shima mataimakin babban daraktan na mussaman, Dr. Sani Dogon Daji, ya ce wannan aiki zai taimaka wajan samawa matasa aiki yi a fadin kasar.

Hakan dai na nuni da cewar ita ma Najeriya a shirye ta ke ta nunawa duniya ta bi sahun shirin samar da tsaftataccen muhalli da kuma dorewar makamashi.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
XS
SM
MD
LG