Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Sami Guraban Matasa 100 a Shirin YALI


Tambarin YALI
Tambarin YALI

Kimanin matasa yan Najeriya su 100 ne a bana suka sami damar zuwa kasar Amurka a shirin nan na mandela washington fellow, YALI, shirin da shugaba Obama ya kirkiro don Horas Da Matasa Manyan Gobe na Afirka, yana dora matasa kan turbar ci gaba ta hanyar ilmantarwa, horaswa kan shugabanci da kuma mu'amala.

Jakadan Amurka a Najeriya James F. Entwistle, ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda yaga matasan yan Najeriya guda 100 na ta zumudi da dokin tafiya Amurka a shirin nan na horas da matasa da Amurka ke daukar nauyi duk shekara wato YALI.

Entwistle ya bayyana gamsuwarsa kan yadda matasan baya suka ci moriyar wannan shiri, kuma suke bayar da gudunmawarsu a sassa daban daban na Najeriya, a watan Disambar da ta wuce ne matasan da suka amfana da wannan shiri suka kai gudunmawar kayan agaji da ya hada da Tufafi da Barguna a sansanonin yan gudun hijira dake Maiduguri.

Jakadan ya kuma yi tsokaci kan dalilan da yasa aka kirkiro wannan shiri, inda yace wannan shirin horaswa na Mandela Washington Fellows ga matasan Afirka, wani kokarin shugaba Barack Obama ne na kyautata makokamar Afirka, bisa gamsuwa da shirin ne yasa aka kara adadin mahalarta a bana daga 500 zuwa 1000 a wannan shekara.

Fadar White House ta kirkiri wannan shiri ne bisa yin na’am da irin rawar da matasan Afirka ke takawa na karfafa turakun tsarin dimokaradiya da habaka tattalin arziki da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.

Balarabe B Isma’il, dan asalin jihar Kano ne da ya samu shiga cikin wannan shiri, inda yace, “zanje Jami’ar jihar Ohio dake Columbus, kuma ina godiya ga gwamnatin Amurka da kuma dukkannin wadanda sukayi addu’a da bayar da gudummawa wajen samun wannan nasara.”

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG