Accessibility links

Najeriya ta Samu Gagagrumar Nasara a Wannan Shekarar a Kwallon Kafa


Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagles" a filin wasa na kasa dake Abuja, inda aka lallasa 'yan Ethiopia da ci 4 da babu, lahadi 27 Maris, 2011

Skekarar 2013 ta kawo wa Najeriya gagarumar nasara a wasan kwallon kafa

Wannan shekarar ta kawo wa Najeriya gagaruman nasarori yayin da ta ci kofin duniya da na nahiyar Afirka na matasa da na manyan ‘yan wasa.

A watan Fabrairu babbar kungiyar kwallon wasan kafar Najeriya da aka fi sani da suna Super Eagles ta lashe kofin kasa da kasa na nahiyar Afirka karo na uku yayin da ta doke kungiyar Burkina Faso da ci daya da nema a Johannesburg a Afirka Ta Kudu.

A karo na hudu Najeriya ta sake lashe kofin duniya na FIFA na matasa masu shekaru kasa da 17 yayin da ta ci kasar Mexico da ci uku da nema a birnin Abu Dhabi dake Hadaddiyar Daular Larabawa ko United Arab Emirates.

Yayin gasar babu wata kasa da ta ci kungiyar kwallon kafan Najeriya ta matasan Golden Eaglets kuma dan wasan Najeriya Kelechi Ihenacho wanda ya saka kwallo sau shida cikin raga shi ne ya zama zakara kuma dan wasa da ya fi kowa kwarewa.
Wani mai nazari kan wasan kwallon a Afirka David Legge yace ‘yan wasan Golden Eaglets su ne suka yi wasa da ya fi burgewa da yadda suke tura ma juna kwallo a Hadaddiyar Daular Larabawa. Yace idan ‘yan kungiyar suka kasance da zama tare zasu iya cin nasara a wasan Olympics na 2016 da kuma wasu wasanni na kasa da kasa nan gaba.

Game da wasan 2014 na cin kofin duniya Najeriya ta maida hankali ne kan kasar Brazil inda za’a yi wasan. Tuni a jadawalin da aka fitar a zagaye na farko an hadata da kasashen Iran da Bosnia-Herzegovina da kasar Argentina wadda ta taba lashe kofin FIFA na duniya har sau biyu.

Wasan na badi shi ne zai zama karo na biyar da Najeriya zata shiga gasar cin kofin duniya kuma wanda ke horas da kungiyar kuma yake shugabancinta, Stephen Keshi, yana cikin kungiyar Super Eagles da ta fara shiga gasar kofin duniya da aka yi a Amurka a shekarar 1994.

Najeriya ta kai rukuni na kasashe 16 a Amurka a shekarar 1994 da wasan da aka yi a shekarar 1998 a Faransa. Ba shakka Keshi zai so kungiyar ta samu nasarar kai ga rukuni na gaba a Brazil. Yace ya yi amanna Keshi zai so Hukumar Kwallon Kafan Najeriya ko NFF ta biya albashinsa kan kari.

Keshi ya sha yin korafin hukumar bata biyanshi yawancin lokuta a shekarar 2013. Biyan masu horas da ‘yan kwallon kasar ya kamata ya zama kudurin hukumar NFF na daya a sabuwar shekara mai zuwa idan har tana son ‘yan wasan su samu gagarumar nasara a shekarar 2014.
XS
SM
MD
LG