Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Son Yin Abin Tarihi


Likitan hakora Dr. James Rolfe, yana duba hakoran wani saurayi a kasar Afghanistan

Dr. Lawal Bakare na HIET Solutions yana son hada mutane dubu 300 domin su goge hakori lokaci guda, su shiga littafin tarihi na Guiness

Najeriyaq zata sake kokarin shiga littafin tarihi na duniya da ake kira "Guinness Book of World Record" a turance, ta hanyar sanya mutane a wurare dabam-dabam su hadu domin goge hakoransu lokaci guda.

Wannan yunkuri, wanda Dr. Lawal Bakare na kamfanin HIET Solutions tare da hadin kan Kungiyar Likitocin Hakora ta Najeriya suka shirya, zai karfafa guiwar tabbatar da cewa jama'a su na kula da hakoransu, a bayan labari mai amfani da haske game da Najeriya da zai haifar a idon duniya.

Ya ce, "Muna son janyo hankali ga bukatar tabbatar da tsabtar hakora. Muna dokin gudanar da wannan abu, har ma mun fara samun goyon baya daga hukumomin gwamnati, yayin da sassan masu zaman kansu suke ba mu kwarin guiwa."

Wannan abu, wanda ba a saka ranar gudanarwa ba, zai kunshi mutane dubu 300, akasarinsu 'yan makaranta wadanda zasu hadu a wurare dabam-dabam a fadin jihar Lagos.

Dr. Bakare yace su na da kwakkwaran dalili na zaben 'yan makaranta. A cewarsa, "muna sane da cewa ana iya cusa ma yaro akida, kuma irin dokin da suke nunawa game da abu irin wannan yana da yawa. Muna son mu ba su damar su shigar da sunayensu cikin tarihi, yayin da a gefe guda zasu koyi darasi mai amfani na kula da hakoransu."

A halin yanzu dai, kasar Indiya ce ta kafa abin tarihi na yawan mutanen da suka hadu domin goge bakinsu lokaci guda, inda a shekarar 2007 mutane dubu dari daya da saba'in da bakwai da uku (177,003) suka taru wajen goge baki.

XS
SM
MD
LG