Hukumar ta tura tawagarta zuwa kasar Saudiyya, wacce ta sami nasarar rage farashin kudin gidaje, kamar yadda marubucin hukumar Mohammed Aja, ya bayyana, ya kuma kara da cewa Najeriya zata sami ragowar kudi Dala Miliyan Goma sha Biyu da Dubu Dari Uku, daga wannan yunkurin.
Jami’in labarum hukumar, Malam Ubamana, ya bayyana cewa hukumar ta fito da wani sabon shiri na lasisi da zai ba Mahajjata dama, wato ba masu Umra kadai ba, wannan karon duk jihar da take a rukuni na A, Alhazanta zasu iya yin aikin Umra, ba kawai aikin Hajji ba. Bugu da kari, hukumar Alhazai ta kara yi masu bayanin cewa akan yadda take kokarin taga ta rage kudin Hajjin bana.
Haka kuma sakataren hukumar Dr Bm Tambuwal, ya ja hankalin kamfanonin kan muhimmancin rikon amana, inda ya bayyana cewa da masu aikin jihohi da masu jirgin yawo duka na cikin wannan sharadi, wato duk wanda ya biya kudinsa, ya sami biyan bukata.
Bana dai Saudiyya ta mayarwa Najriya dukkan kujerun da take bata gabanin aikin fadada Masallacin Haramin Macca.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.
Facebook Forum