Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nauyin Hukunta 'Yan Bindiga Na Kan Gwamnatocin Jihohi Ne - Lai Mohamed


Alhaji Lai Mohammed

A baya-bayan nan ne jam’iyyar PDP mai adawa, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar ta-baci saboda matsalolin tsaro da jam'iyyar ta ce sun yi wa kasar katutu. 

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, Lai Mohammed ya bayyana cewa nauyin hukunta ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ya rataya ne a wuyan gwamnonin jihohin Najeriya ne.

Lai Muhammad ya fadi hakan ne a matsayin martani ga kalaman jam'iyyar adawa ta PDP da ta nemi gwamnatin tarayya ta dauki kwararran matakan hukunta ‘yan bindiga dadi.

Lai Muhammad ya yi kira ga jam’iyyar PDP da ta yi duk mai yiwuwa wajen tuntubar gwamnonin Najeriya kan dalilinsu na rashin hukunta ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da aka kama a baya maimakon daura laifi kan gwamnatin tarayyar kasar.

Minista Lai Muhammad ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, ya na mai jaddada cewa, alhakin hukunta ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane don kudin fansa ba na gwamnatin tarayyar kasar ba ne..

Ya kara da cewa, abin ya rataya ne a wuyan gwamnonin jihohi da suka hada da ‘ya’yan jam’iyya APC mai mulki da ma na jam’iyyar adawa ta PDP dake siyasantar da lamurran tsaro.

Lai Mohammed ya ce furucin nasa na matsayin martani ne ga kalaman jam’iyyar PDP wacce ke sukar gwamnatin da jam’iyyar APC.

A taron manema labarai a ranar Litinin ne jam’iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ba ta gurfanar da 'yan fashi a gaban kotu, tana mai bayyana hakan a matsayin abin takaici da ban mamaki.

Sai dai ministan yadda labarai, Lai muhammad ya bayyana cewa, abin mamaki ne a ce jam'iyyar PDP da ta mulki Najeriya na tsawon shekaru ba ta san cewa nauyin hukunta masu fashi da garkuwa da mutane na kan gwamnatocin jihohi, ba gwamnatin tarayya ba.

Idan ana iya tunawa, a baya-bayan nan ne jam’iyyar ta PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa dokar ta baci saboda matsalolin tsaro da PDP ta ce sun yi wa kasar katutu.

Ta yi kiran ne sakamakon kashe-kashen da 'yan bindiga da mayakan Boko Haram ke aikatawa a arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa maso tsakiya da kuma hare-haren da 'yan bindiga ke kai a kudu maso gabashi.

XS
SM
MD
LG