Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Daliban Kwalejin Afaka Sun Yi Zanga Zanga a Kofar Majalisar Dokokin Najeriya


Hotunan daliban Kwalejin Afaka da aka sace
Hotunan daliban Kwalejin Afaka da aka sace

"Mun zo ne don mu roki gwamnatin su taimaka su kubutar mana da 'ya'yanmu, ai ko dabbarka ce ta bata za ka shiga damuwa, ballantana yaronka da ka haife su." 

Iyayen daliban kwalejin nazarin ilimin gandun daji ta Afaka da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya, sun dunguma zuwa majalisar dokokin kasar a ranar Talata, don nuna fushinsu kan abin da suka kira biris da su da gwamnati ta yi, dangane da batun ceto ‘ya’yansu da aka yi garkuwa da su.

Dalibai 29 suka rage a hannun ‘yan bindigar ya zuwa yanzu, bayan da aka sako 10 daga cikin 39 da aka sace.

"Mun zo ne don mu roki gwamnatin su taimaka su kubutar mana da 'ya'yanmu, ai ko dabbarka ce ta bata, za ka shiga damuwa, ballantana yaronka da ka haifa." Daya daga cikin mahaifan daliban da aka sace Sunday Musa Hai ya ce.

Ya kara da cewa, "tun lokacin da aka kama su daga ranar 11 na watan Maris, ba mu yi bacci ba."

Iyayen daliban kwalejin Afaka da aka sace suna zanga-zanga a gaban majalisar dokokin Najeriya, Talata 4 ga watan Mayu
Iyayen daliban kwalejin Afaka da aka sace suna zanga-zanga a gaban majalisar dokokin Najeriya, Talata 4 ga watan Mayu

Zangar zangar ta hada har da wasu mambobin kungiyar daliban kwalejin, wadanda suka je majalisar dauke da kwalaye da kyallaye da aka rubuta “A ceto daliban Afaka 29.”

Masu zanga zangar sun yi ta rera wakokin neman a kai masu dauki don ganin an kubutar da ‘ya’yan nasu.

Daya daga cikin daliban da ta tsira daga harin wacce ta shiga zanga zangar ta ranar Talata, ta ce har yanzu tana cikin fargabar abin da ya faru saboda harbin bindigogi da ta ji.

"Har yau, ko da tayar mota ce ta fashe, sai gaba na ya fadi, saboda karar bindigogi da na ji a lokacin da aka kai harin." In ji Christiana Gaida.

A ranar 11 ga watan Maris ‘yan bindigar suka shiga kwalejin ta Afaka da ke karamar hukumar Igabi, suka yi awon gaba da dalibai 39, inda suka kutsa da su cikin daji.

Asali daruruwan dalibai maharan suka tattara za su gudu da su daga kwalejin, amma wata arangama da suka yi da jami’an tsaro ta sa abin ya tsaya akan dalibai 39.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai

Kwanaki kadan bayan satar daliban na Afaka, wasu ‘yan bindigar kuma sun sace wasu dalibai a Jami’ar Greenfield mai zaman kanta da ke jihar ta Kaduna inda suka nemi a biya su kudin fansa.

Gazawar hakan ya sa maharan suka kashe biyar daga cikin dalibai 22 da suka sace a jami’ar.

Ita dai gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin ba za ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba, kuma ba za ta biya kudin fansa ba, lamarin da ya haifar da ka-ce-na-ce a jihar ta Kaduna da ma Najeriya baki daya.

XS
SM
MD
LG