Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netherlands Ta Doke Senegal Da Ci 2-0


Netherlands da Senegal
Netherlands da Senegal

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Netherlands ta doke takwararta ta kasar Senegal a wasan farko da aka buga a kasar Qatar

Netherlands ta zura kwallaye biyu cikin minti na karshe ta hannun Cody Gakpo da Davy Klaassen da ya maye gurbinsa, inda suka doke Senegal da ci 2-0 a gasar cin kofin duniya da suka buga a rukunin A a filin wasa na Al Thumama a yau Litinin.

'Yan kasar Holland din, wanda ba su samu damar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018 ba, sun samu nasara ne bayan Gakpo da ke kan gaba ya doke mai tsaron gida Edouard Mendy inda ya kai ga bugun da ya yi da bayan kai.

‘Yan kasar Holland sun bi sawun Ecuador wanda su ma su ka yi nasara a kan Qatar da ci 2-0 a ranar Lahadi, da maki uku, tare da manyan kasashen biyu a ranar Juma’a.

"Wasa ne mai wahala kuma ba mu yi taka-tsantsan da kwallon ba," in ji Gakpo. "Ina ganin za mu iya yin abin da ya fi kyau amma nasarar a fili ta sa mu jin dadi."

"Da muke fili, mun dage wajen neman zura kwallo kuma daga karshe mun samu," in ji shi.

Dan wasan mai shekaru 23, wanda yanzu ya zura kwallaye uku a wasanni hudun da ya buga na kasa da kasa, ya samu damarsu ta farko bayan mintuna hudu, amma ya yi kokarin turawa Steven Bergwijn kwallo maimakon ya zura a raga.

Hakan ya biyo bayan bugun kwallo da ka da Daley Blind ya yi da nisa kafin Steven Berghuis ya kare Bergwijn sannan ya turawa De Jong kwallon.

Dan wasan tsakiyar ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya saki kwallon, duk da haka, an takawa kokarinsa birki.

Zakarun na Afrika sun yi rashin dan wasan da ya ji rauni Sadio Mane, kuma bai samu bugawa ba sai cikin minti na 65, lokacin da Boulaye Dia ya yi kokarin lallasa mai tsaron gida Andries Noppert. Wannan ne ya kasance wasansa na farko a kasar Holland.

Senegal ta fi samun damar wasa da kwallo a karo na biyu amma duk da karfafawa da suka dinga samu daga masu goyon bayansu, ba su samu zura kwallo a raga ba.

Abun da kuma ya kara dagula lamarin shine cire Cheikhou Kouyate yayin da ji rauni kafin Gakpo ya kutsa kai ya kwace kwallon farko.

A yanzu haka dai an kasa doke ‘yan kasar cikin wasanni 16 da suka buga a karkashin koci Louis van Gaal.

Sun kuma kafa tarihin na rashin doke su a wasansu na farko a gasar cin kofin duniya da aka yi tun a shekarar 1938.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG