Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Sarkin Katsina Maradi Ali Zaki Ya Rasu


Sultan Ali Zaki
Sultan Ali Zaki

Daya daga cikin sarakunan Musulmi 4 Ali Zaki na Katsina Maradi ya rasu kamar yadda hukumomin jihar Maradi suka tabbatar wa manema labarai.

Sultan Ali Zaki ya kasance daya daga cikin Sultan 4 ko sarkin Musulmi na Nijar, bayan Sultan na Zinder, Agadez da Dosso.

Kuma yana mulkin masarautar Katsina Maradi da ke kasancewa cibiyar tattalen arzikin Jamhuriyar Nijar kuma jiha mafi yawan al'umma a kasar.

Muryar Amurka ta tuntubi Alhaji Salisu Issa, wani Dan jarida dake Maradi ya ce Sarkin ya dade yana jinya kafin Allah ya yi masa rasuwa.

Ita dai masarautar Maradi na kasancewa daya daga cikin manyan masarautun kasar da ta yi suna sosai a karni na 18 a lokacin mulkin Bawa Jan Gorzo.

Har izuwa yanzu, bayan kira da sanar da manema labarai da rasuwar sultan na Maradi Ali Zaki da ma'aikatar gwamnan jihar Maradi ta yi, ba wata sanarwa da hukumomi na jihar ko na kasar suka yi game da wannan rashin da kasar tayi.

Saurari cikakken rahaton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG