Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Za Ta Fara Cin Tarar Masu Batanci A Kafafen Sada Zumunta


.
.

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amincewa gwamnatin kasar ta soma zartar da dokar hukuncin biyan tara ga mutanen da aka kama da laifin cin zarafi ko yiwa wani kazafi ta yanar gizo a maimakon hukuncin zaman wakafi da aka saba yankewa irin wadanan mutane a can baya

NIAMEY, NIGER - Matakin da cibiyar ‘yan jarida ta ce ya yi daidai ganin yadda abin zai bada damar fayyace ‘yan jarida da masu rubutun batanci a kafafen sada zumunta.

Kudirin dokar da gwamnatin ta Nijar ta aika wa majalisar dokokin kasa na cewa daga yanzu duk wanda ya yi amfani da yanar gizo don yada rubutu ko muryoyi ko hotuna ko bidiyo ko zanen dake kunshe da bayanan gwada wariyar launin fata ko cinhanci ko kabilanci ko bambancin addini ko kuma nuna kyamar baki da dukkan wasu abubuwan da zasu haddasa tashin hankali a tsakanin ‘yan kasa zai biya tarar kudade.

An kayyade tarar ta kudade da suka kama daga million 5 na cfa zuwa million 10 sannan za a hana wanda aka kama zama a kasar har inna ma sha Allahu. Mai shara’a Maman Sani Jdibaje na cikin darektocin ma’aikatar shara’a ta kasa ya shaida haka.

A yayin kuri’ar da aka yi daukacin ‘yan majalisar ne suka yi na’am da matakin gwamnatin ta Nijar. Honorable Kalla Moutari shugaban kwamitin dake kula da sha’anin doka a majalissar dokokin kasa Commission CAGI na daga cikin wadanda suka yi na’am da hakan.

Daga lokacin soma zartar da dokar hukunta mutanen da aka kama da laifin cin zarafi a kafafen sada zumunta wato 2019 kawo yau dimbin ‘yan adawa ne da hukumomi suka kulle a gidan kaso mafari kenan ‘yan majalisa na jam’iyun hamayya suka yi na’am da gyaran fuskar da gwamnatin ta gabatar inji Honorable Soumana Hassane koda yake ba girin-girim ba tayi mai inji shi.

A ra’ayin sakataren watsa labaran cibiyar ‘yan jarida Souleymane Oumarou Brah maye gurbin hukuncin zaman wakafi da biyan tara mataki ne da zai bada damar bambanta rubutun ‘yan jarida da na wadanda ke fakewa da kafafen sada zumunta don cimma wata muguwar manufa.

A shekarar 2019 ne gwamnatin Nijar ta kafa dokar hukunta masu amfani da kafafen sada zumunta bayan la’akari da abinda ta kira yawaitar cin zarafin manyan mutane a irin wadanan dandalin mahawara yayinda ‘yan hamayya ke ganin abin a matsayin wani yunkurin rufe bakin jama’a.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Za Ta Fara Cin Tarar Masu Batanci A Kafafen Sada Zumunta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG