Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NJC Ta Ba Da Shawarar Nadin Alkalai, Jami’an Shari’a 37 A Najeriya


Babban alkalin Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko.

Majalisar harkokin shari’a a Najeriya ta duba jerin sunayen alkalai da ma’aikatan shari’a da kwamitin daukan aikinta ya gabatar mata kuma ta yanke shawarar amincewa da jami’ansu 37.

Majalisar ta yanke wannan shawarar ne a taronta karo na 95 na ranakun 15 da 16 ga watan Satumbar shekarar 2021 inda hakan ke nufin ma’aikatan shari’ar 37 sun sami nasarar shugabancin kotuna a matakin jihohi da kuma sauran jami'an shari'a a matakin tarayya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin sanarwar da daraktar yadda labaran majalisar, Soji Oye, ya fitar a yau Lahadi.

Ma’aikatan aikin shari’ar zasu rika aiki ne a karkashin gwamnonin jihohin su don tafiyar da harkokin shari’a a can din.

A babbar kotun jihar Kogi an nada mai shari’a Richard O. Olorunfemi, ya shugabance ta.

A babbar kotun jihar Edo mai shari’a, oe Itsebaga Acha, a Ondo mai shari’a, Akintoroye Williams Akin, a birnin tarayya Abuja, mai sharia, Husseini Baba Yusuf, Akwa-Ibom mai shari’a, Ekaette Francesca Fabian-Obot, Ekiti mai shari’a, Justice J. O. Adeyeye.

Sai kuma grand Kadi na jihar Yobe, Kadi Baba Gana Mahdi, jihar Bauchi, Umaru Ahmad Liman.

Sauran sun hada da shugaban kotun daukaka karar jihar nasarawa, mai shari’a Osagede Osado Emmanuel, jihar Oyo, mai shari’a Mashud Akintunde Akinfemi Abass, Kogi Siyaka Momoh Jimoh Usman, da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG